Buhari ya ware N47bn a kasafin kudin bana domin farfado da 'Nigeria Air'

Buhari ya ware N47bn a kasafin kudin bana domin farfado da 'Nigeria Air'

Gwamnatin tarayya ta ware biliyan N47 a cikin kasafin kudin shekarar 2019 domin farfado da masana'antar sufurin jirgin sama ta kasa (Nigeria air).

Batun ware makudan kudin na zuwa ne bayan majalisar zartarwa ta kasa (FEC) ta bayyana dakatar da shirin farfado da masana'antar har sai baba-ta-gani.

Hadi Sirika, minsitan harkokin jiragen sama, ne ya sanar da hakan a ranar Litinin a cikin wani jawabi da James Odaudu, mataimakin darektan yada labarai a ma'aikatar sufuri, ya fitar.

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika bukatar neman ware kudaden domin fara aikin tayar da masana'antar a cikin kasafin shekarar 2019 kuma majalisa ta amince da hakan," a cewar sa.

Buhari ya ware N47bn a kasafin kudin bana domin farfado da 'Nigeria Air'

Hadi Sirika
Source: Depositphotos

A wani jawabi da ya gabatar a taron masu ruwa da tsaki da aka yi a watan Nuwamba na shekarar 2018, Sirika ya bayyana cewar ana bukatar kudi $155m domin gudanar da aikin dawo da 'Nigeria airways'.

DUBA WANNAN: Kotu ta kara kwace kujerar majalisar wakilai daga hannun APC, ta umar INEC ta bawa PDP

Idan aka mayar da kudin zuwa Naira a kan farashin canjin kowacce $1 a kan N360, adadin kudin zai kasance biliyan N47.43.

Jaridar TheCable ta ce wani bincike da ta gudanar ya nuna mata cewar an taba ware wa aikin biliyan N8.7 a baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel