Hukumar NDLEA za ta gudanar da bincike akan sabbin manyan sakatarorin gwamnatin Kano - Ganduje

Hukumar NDLEA za ta gudanar da bincike akan sabbin manyan sakatarorin gwamnatin Kano - Ganduje

Manufar cimma burin gwamnati da yiwa al'umma hidima ya sanya gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya nada sabbin manyan sakatarori 36 na ma'aikatun gwamnati kamar yadda shugaban ma'aikatan jihar Auwal Na'iya ya bayyana.

Biyo bayan wannan nadi na mukami, gwamna Ganduje ya gabatar da jerin saunyen sabbin sakatarorin 36 zuwa ga hukumar yaki da sha da kuma safarar miyagun kwayoyi watau NDLEA domin gudanar da bincike a kan koshin lafiyar hankulan su.

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje
Source: Twitter

Gwamna Ganduje ya yi gargadi sabbin sakatarorin da cewa duk wanda hukumar ta kama sa rashin lafiyar tabin hankali ko kuma bincike ya tabbatar da alakar sa da miyagun kwayoyi zai yi asarar sabon mukamin sa yayin da gwamnatin sa ta shafa bakin kwalli na kyamatar muggan kwayoyi.

A cewar gwamna Ganduje da ake yiwa lakabi da Khadimul Islama, gwamnatin sa ta dauki wannan salo na tabbatar da koshin lafiyar hankulan masu rike da madafan iko a gwamnatin sa domin tabbatar da ingancin mai hadi da nagarta wajen sauke nauyin da rataya a wuyansu.

KARANTA KUMA: Zan kawo karshen matsalar tsaro a jihar Zamfara - Mutawalle

Gwamnan wanda ya yi furucin hakan a ranar Lahadin da ta gabata bayan da kwamishinan shari'a kuma lauyan koli na jihar Ibrahim Mukhtar ya rantsar da sabbin manyan sakatarorin 36, ya nemi su jajirce wajen bayar da muhimmanci a fagen samar da kudaden shiga domin samun damar biyan ma'aikatan jihar mafi karancin albashi na Naira dubu talatin.

Gwamna Ganduje bayan shawartar manyan sakatarorin akan tsayuwa bisa gaskiya yayin sauke nauyin da rataya a wuyan su, jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, nadin sabbin mukaman gwamnatin ya kunshi Mata 11 da kuma Maza 25.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel