Abun al’ajabi: An yiwa yan majalisa masu barin gado gwanjon kayayyakin ofis na miliyan 3 akan N367,479

Abun al’ajabi: An yiwa yan majalisa masu barin gado gwanjon kayayyakin ofis na miliyan 3 akan N367,479

Hukumar gudanarwa na majalisar dokokin kasa ta yiwa yan majalisa masu barin gado gwanjon kayayyakin ofis a farashi mai rahusa.

Wasu daga cikin yan majalisan da basu yi nasaran komawa ba sun soma kwasan kayayyakin ofis cikin motoci.

Ko da yake wasu yan majalisar sun yi kyautar kayayyakin ga hadimansu da magoya bayansu, wasu kuma sun gwamnaci su siyar ga masu siya a harabar majalisar dokokin kasa.

Abun al’ajabi: Hukumar majalisa na yiwa yan majalisa masu barin gado gwanjon kayayyakin ofis

Abun al’ajabi: Hukumar majalisa na yiwa yan majalisa masu barin gado gwanjon kayayyakin ofis
Source: UGC

Wasu ma’aikata a majalisan dokoki sun sha mamaki akan lamarin, musamman bisa karamcin farashin da aka bada kayayyakin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya sanya hannu a kasafin kudin 2019

A wani takardan da manema labaranmu ya gano, an siyar da kayayyakin ofis din akan kudi naira 367,479.33.

Duk mammba da zai dauki gaba daya kaya 11 zai biya #349,970,50, da N17,498.83 a matsayin haraji (VAT).

Majiya sunyi jimlan kudin kayayyakin a kasuwa inda farashinsu ya kama fiye da naira miliyan uku.

Ga rabe-raben farashin da yan majalisa suka siya wasu daga cikin kayayyakin

1. Samsung double door refrigerator - N25,000

2. HP Envy Core 13 - N49,000

3. Apple Ipad Air computer - N41,980

4. LED TV Samsung UA4600AR 50 - N59,500

5. Shredding machine - N19,800

6. Water dispenser with bottle - N8,990

7. Photocopying machine Sharp Copier AR 6021 - N57,172.00

8. Scanner HP Scanjet Pro 3900 Fi - N20,130.00

9. HP Laserjet Pro M201 - N10,038.00

10. Desktop Computer Model Envy 23″ Touch screen; and Suit hanger - N1,900.00.

Ga ainahin farashin kayayyakin a kasuwa:

1. Led television - N300,000

2. HP Envy Core 13 - N400,000

3. HP Desktop Envy23″ - N420,000

4. Samsung double door refrigerator - N315; 000

5. Sharp Copier AR6023 - N380; 000

6. HP Laserjet M201 dw - N120,000

7. HP Scanjet Pro 3500F1 - N195,000

8. Cway water dispenser - N50,000.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel