Yanzu Yanzu: Buhari ya sanya hannu a kasafin kudin 2019

Yanzu Yanzu: Buhari ya sanya hannu a kasafin kudin 2019

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kasafin kudin 2019 a safiyar yau Litinin, 27 ga watan Mayu.

An gudanar da bikin sanya hannun ne a ofishin Shugaban kasar da misalin karfe 11 na safe.

Tuni dai kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan kasafin kudi, Danjuma Goje, Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Udoma Udo Udoma, babban mai ba Shugaban kasa shawara akan harkokin majalisar dokoki, Ita Enang duk sun hallara a fadar shugaban kasar.

Sauran wadanda suka halaarci taron sun hada da minister kudi, Zainab Ahmed, ministan labarai, Alhaji Lai Mohammed, Gwamnan babban bankin Najerya, Godwin Emefiele, Shugaban ma’aikata, Abba Kyari da babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

KU KARANTA KUMA: Ahmed Lawan yayi magana kan albashin miliyan 13.5 da sanatoci ke kwasa duk wata

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa, Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa kuma dan takarar kujerar Shugaban majalisar dattawa ta tara, Sanata Ahmed Lawan, ya bayyana cewa idan har ya zama Shugaban majalisar zai wanzar da kyakkyawar mu’amala tsakanin majalisa da bangaren zartarwa.

Lawan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 25 ga watan M,ayu a yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja.

Sanatan wanda shi ne dan takarar da jam’iyyar APC da jiga-jigan ta, da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ke goyon baya don ganin ya zama shugaban majalisa, ya ce ya yi imani da cewa yawan samun sabani da sa-in-sa tsakanin majalisa da bangaren zartarwa, ba shi da alfanu , domin kasar ce da al’ummar da ke cikin ta abin ke rika shafa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel