Ahmed Lawan yayi magana kan albashin miliyan 13.5 da sanatoci ke kwasa duk wata

Ahmed Lawan yayi magana kan albashin miliyan 13.5 da sanatoci ke kwasa duk wata

- Dan majalisa mai wakiltan Arewacin Yobe a majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan, yace babu sanatan da ke cin albashi mai kauri

- Sanata Lawan yace kowani sanata na tafiya gida da kimanin naira miliyan daya ne a wata da kuma alawus na wasu ayyuka

- Sanata Lawan yana takaranr mukamin shugaban majalisar dattawa

Sanata Ahmed Lawan yayi bayani akan naira miliyan 13.5 da ake biyan kowani mutum guda daga cikin sanatoci 109 a matsayin albashi, yace mafi girman kaso na kudaden daga alawus ne.

Lawan, wanda ke takaran shugabancin majalisar dattawa a majalisar dokokin kasar na tara, yace baza a rage yawan albashin ba idan ya zama shugaban majalisa.

Ahmed Lawan yayi magana kan albashin miliyan 13.5 da sanatoci ke kwasa duk wata

Ahmed Lawan yayi magana kan albashin miliyan 13.5 da sanatoci ke kwasa duk wata
Source: Facebook

A cewar dan majalisar mai wakiltan Arewacin Yobe, babu wani abu mai kama da albashi mai tsoka da ake biyan sanatoci saboda kowannensu na daukan naira miliyan daya ne a wata tare da kuma alawus na sauran ayyuka.

KU KARANTA KUMA: Ba zan yi sa-in-sa da Buhari ba idan na zama Shugaban majalisa – Ahmed Lawan

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa kungiyar matasan Arewa bata amince da zabin Sanata Ahmed Lawan a matsayin shugaban majalisar dattawa ba, inda take cewa majalisar zata zama tamkar marasa tasiri.

Kungiyar AYCF din tace amincewa a daura lawan a kujeran zai dauke martabar yankin Arewa a sanadiyan mutum daya, wanda baya iya tsayawa ya yanke shawara ga Arewa bisa bukatunta.

Ta bayyana cewa tunda an yanke shawaran cewa shugaban majalisa zai zo daga yankin Arewa maso gabas, dole a bari yankin ta yanke shawara akan dan takara da yafi cancanta, “wanda ba kowa ba illa Ali Ndume”.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel