Ba zan yi sa-in-sa da Buhari ba idan na zama Shugaban majalisa – Ahmed Lawan

Ba zan yi sa-in-sa da Buhari ba idan na zama Shugaban majalisa – Ahmed Lawan

Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa kuma dan takarar kujerar Shugaban majalisar dattawa ta tara, Sanata Ahmed Lawan, ya bayyana cewa idan har ya zama Shugaban majalisar zai wanzar da kyakkyawar mu’amala tsakanin majalisa da bangaren zartarwa.

Lawan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 25 ga watan M,ayu a yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja.

Sanatan wanda shi ne dan takarar da jam’iyyar APC da jiga-jigan ta, da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ke goyon baya don ganin ya zama shugaban majalisa, ya ce ya yi imani da cewa yawan samun sabani da sa-in-sa tsakanin majalisa da bangaren zartarwa, ba shi da alfanu , domin kasar ce da al’ummar da ke cikin ta abin ke rika shafa.

Ba zan yi sa-in-sa da Buhari ba idan na zama Shugaban majalisa – Ahmed Lawan

Ba zan yi sa-in-sa da Buhari ba idan na zama Shugaban majalisa – Ahmed Lawan
Source: UGC

Ya kara da cewa shekaru hudu da aka yi ana mulki tsakanin 2015 zuwa 2019, bangaren shugaban kasa bai samu kyakkyawar mu’amala da shuagabancin majalisar dattawa ba.

Ya ce a bangarorin biyu kowa ya sha kin amincewa a kan wasu batutuwa.

Sai dai kuma shi ya na da tabbatacin cewa bai ga dalilin da zai rika sa-in-sa da bangaren gwamnati ba, matsawar dai kowa a tsaya a matsayin sa.

Ya ce mu’amala iri biyu ce tsakanin majalisa da bangaren mulki. Ko dai a yi kyakkyawa ko kuma a yi mai tsami.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An shiga halin dar-dar a Jos yayinda hukumomin tsaro suka tura karin jami’ai

Ya ce tabbas akwai inda bangaren gwamnati za su bijiro da wasu batutuwa masu kyau, amma majalisa kuma za ta yi musu duba da irin ta su fahimtar a bisa yadda doka ta shimfida komai.

Lawan ya ce ba zai yi ja-in-ja ko sa-in-sa da bangaren shugaban kasa ba. Sai dai ya kara da cewa ba kuma zai zama rakumi da akalar da za a rika jan sa sakaka ba.

Daga nan sai Lawan ya kara jinjina goyon bayan sa ga Shugaba Buhari da kuma Gwamnatin sa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel