Yanzu Yanzu: An shiga halin dar-dar a Jos yayinda hukumomin tsaro suka tura karin jami’ai

Yanzu Yanzu: An shiga halin dar-dar a Jos yayinda hukumomin tsaro suka tura karin jami’ai

An shiga halin fargama a kewayen Dutse Uku, Cele Bridge da kuma Rikkos da ke karamar hukumar Jos ta arewa a jihar Jos yayinda muka samu rahoton da ke ikirarin cewa matasa a yankin na kone-konen gidaje, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, baabu tabbaci kan abunda ya haddasa rikici a yankin amma rahotanni sun nuna cewa an gano gawar wani matashi a yankin Anguwan Damisa da ke Dutse Uku.

Wani idon shaida ya tabbatar da cewa an tura jam’an tsaro na Operation Safe Haven yankin domin su kwantar da lamarin inda ya kara da cewa, “a yanzu haka jami’an tsaro sun yi tsaye a tsakanin Dutse Uku da Anguwan Damisa; sannan akwai jami’an Silbu defense da kuma na ofishin yan sandan Nasarawa Gwom.

Yanzu Yanzu: Ana zaman dar-dar a Jos yayinda hukumomin tsaro suka tura karin jami’ai

Yanzu Yanzu: Ana zaman dar-dar a Jos yayinda hukumomin tsaro suka tura karin jami’ai
Source: Depositphotos

An tattaro cewa Dutse Uku, wani gari da ke iyaka da garuruwan Musulmai da Kiristoci da dama ya shiga labarai yan watanni da suka gabata saboda rikici.

KU KARANTA KUMA: Ministoci masu barin ofis da Gwamnoni su na harin mukamai a Gwamnatin Tarayya

Gano wata gawa da aka yi a wani rijiya a watan Maris ya haddasa tsoro a yankin lokacin da matasa suka fara shirya harin ramuwa kafin daga bisani jami’an tsaro su tarwatsa su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Online view pixel