Ministoci masu barin ofis da Gwamnoni su na harin mukamai a Gwamnatin Tarayya

Ministoci masu barin ofis da Gwamnoni su na harin mukamai a Gwamnatin Tarayya

Ministocin da ke shirin barin ofis da kuma gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki su na ta kokari wajen ganin mutanensu sun samu shiga cikin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da za a kafa.

A gobe da daddare ne wa’adin shugaban kasa Buhari zai kare, inda zai soma wa’adin sa na karshe a Ranar Laraba. Kamar yadda mu ka samu labari, Ministoci masu-ci su na kokarin ganin sun zarce.

Haka zalika a wani bangaren kuma, Gwamnonin jam’iyyar APC da su ka samu tazarce su na kokarin ganin cewa su ne su ka bada sunayen wadanda za a nada Minista daga jihohin su a wannan karo.

Wannan zai ba wadannan gwamnoni dama su kara karfi a jam’iyya idan ya zama Yaran su ne su ke rike da kujerar Minista. Mu na kuma jin kishin-kishin cewa wannan karo za a nada Ministoci da wuri.

KU KARANTA: A kwana a tashi: Wata rana zan yi mulkin Najeriya – Gwamnan Imo

Majiyar mu ta bayyana cewa har yanzu ba a san inda shugaban kasar ya dosa ba a game da nadin sababbin Ministocin a yayin da wasu manyan jam’iyya su ke ta faman zuwa neman alfarma wajensa.

Akwai jihohin da siyasar tayi zafi a sakamakon gwamnonin da ke shirin barin-mulki da kan su ne ke harin kujerar Minista a 2019. A irin wannan jihohi APC ta fadi zabe ko wa’adin gwamna ya cika.

Labaran da mu ke samu sun bayyana cewa manyan APC su na ta shirya taro iri-iri a game a kan nadin Ministocin da za ayi. Su dai Ministocin da ke kan kujera yanzu, su na sa ran cewa za a koma da su.

The Nation ta rahoto cewa masu neman Minista a Najeriyar sun fara ganawa da na-hannun daman shugaba Buhari domin a dafa masu. Sai dai babu tabbacin matakin da shugaban kasar zai dauka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel