Ban da niyyar barin APC don mun rasa shari’a a Kotu - Yari

Ban da niyyar barin APC don mun rasa shari’a a Kotu - Yari

Mun ji cewa gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Abubakar Yari ya bayyana cewa ba zai bar jam’iyyarsa ta APC ba, duk da kalubalen da su ke fuskanta a halin yanzu bayan hukuncin da kotun koli tayi.

Kamar yadda labari ya zo mana, gwamnan yace ba zai tsere ya bar jam’iyyar APC ba domin da su aka kafa ta. Gwamnan ya bayyana wannan ne a karshen makon nan a Mahaifarsa ta Talata Mafara.

Gwamnan mai shirin barin-gado yake cewa wasu daga cikin Magoya bayansa sun fara kira da ya sauya-sheka amma yace bai da niyyar canza jam’iyya a sakamakon karbe kujerunsu da aka yi a kotu.

Ban da niyyar barin APC don mun rasa shari’a a Kotu - Yari

Gwamnan Zamfara ba ya tunanin ficewa daga Jam’iyyar APC
Source: Facebook

Babban gwamnan yake cewa shi da irin su tsohon gwamnan Legas Babatunde Fashola; da Rauf Aregbesola na jihar Osun; da kuma gwamna Rochas Okorocha; da Kayode Fayemi su ka kafa APC.

A dalilin haka ne gwamnan yace ba zai bar ginin da yayi ya rushe ba saboda kotu ta ba jam’iyyar PDP nasara a zaben 2019. Gwamnan mai shirin barin-gado yace yanzu su ka fara tafiyar APC a kasar.

A Ranar Juma’ ne kotun koli ta yanke hukunci a game da dambarwar da ake tayi a jihar Zamfara inda aka rushe duk nasarar da jam’iyyar mai mulki ta samu saboda rashin shirya zaben fitar-da-gwani.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel