Dambarwar masarautar Kano: An bukaci Sarki Muhammadu Sunusi yayi murabus

Dambarwar masarautar Kano: An bukaci Sarki Muhammadu Sunusi yayi murabus

Hadaddiyar kungiyar yan Arewa masu rajin samar da cigaba da dimukradiyya, NADP ta soki lamirin mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, inda ta nemi yayi gaggawar yin murabus daga sarautar Kano don kare mutuncin masarautar.

Kungiyar ta bayyana haka ne a ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu a karshen taronta daga gudanar a babban birnin tarayya Abuja, taron daya samu halartar wakilanta daga jahohi 18 a Arewacin Najeriya inda suka tattauna batun matsalar tsaro a Arewa da kuma rikicin masarautar Kano.

KU KARANTA: Rikicin siyasar Zamfara: Kanin Sheikh Ahmed Gumi ya zama dan majalisar tarraya a PDP

Dambarwar masarautar Kano: An bukaci Sarki Muhammadu Sunusi yayi murabus

Dambarwar masarautar Kano: An bukaci Sarki Muhammadu Sunusi yayi murabus
Source: Twitter

A karshen zamanta, shugaban kungiyar, Dakta Abba Gwarzo ya sanar da matsayin kungiyar game da abubuwan da suka tattauna, inda suka yi kira ga gwamnatin tarayya data kafa wata rundunar tsaro ta musamman data kunshi jami’ai daga dukkanin hukumomin tsaro da zasu dinga sintiri a jahohin da lamarin yafi kamari, Zamfara, Kaduna da Benuwe.

Haka zalika kungiyar ta jinjina ma namijin kokarin da gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yayi na nada sabbin sarakunan gargajiya guda hudu masu daraja ta daya a jahar Kano, na Rano, Bichi, Karaye da Gaya.

Kungiyar tace matakin yayi daidai da gwagwarmayar da talakawa ke yin a samun yanci daga sarakuna tare da kawar da mulkin zalunci tun a shekarar 1950, don haka suka ce matakin yayi daidai saboda zai kara hadin kai tsakanin jama’a, tare da kawar da duk wani rikici a jahar Kano.

Daga karshe Dakta Gwarzo yayi kira ga yan Najeriya dasu yi tir da Allah wadai da kokarin da Sarkin Kano yake yi na tayar da zauni tsaye a jahar da ka iya tayar da rikici a jahar, hakanan wasu daga cikin mahalarta taron sun yi kira ga Sarkin da yayi murabus don kare mutuncin masarautari.

Wakilan sun bayyana haka ne duba da zarge zargen almubazzaranci dake hukumar yaki da rashawa ta jahar Kano take yi masa, bugu da kari sun bayyana bacin ransa da yadda Sarkin yake nuna bangaranci a siyasar Kano.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel