Abin da ya sa manyan Mala’un Gari ba su tare da ni - Gwamnan Imo Okorocha

Abin da ya sa manyan Mala’un Gari ba su tare da ni - Gwamnan Imo Okorocha

Mun samu labari cewa gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo yayi magana bayan an hana sa satifiket din da ke nuna cewa ya samu nasara a zaben Sanatan da yayi a babban zaben shekarar nan.

Rochas Okorocha ya fito ya bayyana cewa wadanda su ka shirya masa wannan tuggu, su na kara kai shi daf da kujerar shugaban kasar Najeriya ne. Gwamnan ya bayyana wannan ne a wajen taron coci.

A jiya Lahadi 26 ga Watan Mayun gwamnan ya halarci hudubar cocinsa na karshe a gidan gwamnatin jihar Imo inda yayi kaca-kaca da Abokan hamayyar sa, yana mai masu barazanar zuwa gidan yari.

Gwamnan mai shirin barin-gado yake cewa: “Masu burin su ga na tafi gidan yari, sai sun yi zaman kaso kafin ni…”

Gwamnan ya kuma bayyana cewa babu ‘dan siyasar da ke shan suka a Najeriya kamar sa. “Bari in fada maku, babu ‘Dan siyasar da ke gamuwa da suka a Najeriya yau iri na…Manyan kasar nan ba su tare da ni ko kadan, domin na canza irin kidar gwamnati”

KU KARANTA: INEC ta hana a ba Gwamna Okorocha takardar shaidar lashe zabe

Abin da ya sa manyan Mala’u ba su tare da ni - Gwamnan Imo Okorocha

Gwamnan Imo Okorocha yace wata rana zai yi mulkin Najeriya
Source: Twitter

…Duk kuma wani shiri da ake yi na hana ni zama Sanata bai zai kai ko ina ba. Har yanzu ina fafutukar ganin na tafi Majalisar Dattawa. Sama da mutum 30 su ke kara ta a Kotu, amma duk da haka zan yi nasara.”

“Masu yi mani wannan makirci, su na yi mani tanadin gaba ne! Na fada a kan mimbari cewa zan zama shugaban kasar nan wata rana.”

Gwamnan ya kuma ce kusan kashi 95% na mutanen Imo ba su fahimci irin tsarin mulkin sa ba;

“Mutane kadan su ka gane cewa alheri na ke neman al’umma da shi kuma na sa Jihar Imo zuciya ta. Nayi bakin kokari na a cikin shekaru 8, amma ban taba saba wata doka ba.”

“Na bar Jihar Imo a halin da ya fi yadda na karbe ta kuma na shiga sabon tarihin jihar, ina mai alfahari da aikin da na yi”. Gwamnan ya karasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel