Luguden wuta: Dakarun soji sun kashe 'yan bindiga da dama a harin dajin Doumbourou

Luguden wuta: Dakarun soji sun kashe 'yan bindiga da dama a harin dajin Doumbourou

Rundunar sojin sama (NAF) ta ce rundunar atisayen 'HADARIN DAJI' ta lalata wani sansanin 'yan bindiga tare da kashe da dama daga cikinsu a wani hari da suka kai a dajin Doumbourou dake jihar Zamfara.

Ibikunle Daramola, kwamanda a rundunar NAF mai rike da mukamin darektan yada labarai da hulda da jama'a, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja. Ya ce dakarun NAF sun kai harin ne ranar Asabar.

"An kaddamar da harin ne ranar Asabar, 25 ga watan Mayu bayan mun samu wasu bayanan sirri da suka tabbatar da cewar 'yan bindigar na boye a dajin. Bayanai sun tabbatar mana cewar hatta shugaban 'yan bindigar da ake kira 'Dangote' na da bukka a cikin dajin.

Luguden wuta: Dakarun soji sun kashe 'yan bindiga da dama a harin dajin Doumbourou

Jirgin yakin rundunar NAF
Source: Twitter

"Bayan tabbatar da bayana da muka samu, jirginmu na yaki 'Alpha Jet' ya kai hari tare da lalata sansani da kuma kashe 'yan bindiga fiye da dozin biyu," cewar Daramola

DUBA WANNAN: Mayakan Boko Haram sun kashe sojoji 25 a wani harin kwanton bauna

Daramola ya kara da cewa rundunar NAF, tare da hadin gwuiwar ragowar jami'an tsaro, zata cigaba da gudanar da atisaye domin karkade birbishin 'yan bindagar dake yankin arewa maso yamma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel