Duk lokacin da nayi magana sai a ce na cika surutu, ina sukar gwamnati - Aisha Buhari

Duk lokacin da nayi magana sai a ce na cika surutu, ina sukar gwamnati - Aisha Buhari

Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta koka a kan yadda duk lokacin da ta fadi matsalar gwamnati sai wasu jama'a suke korafi da yamudidi da ita a kan cewar ta cika surutu tare da zarginta da sukar gwamnati.

Uwargida shugaban kasar ta bayyana hakan a ranar Asabar yayin wani taro da tayi da mata a fadar shugaban kasa ranar Asabar, inda ta soki shirin bayar da tallafi na gwamnatin tarayya (SIP) wanda Maryam Uwais ke jagoranta.

Da take koka wa a kan yadda shirin na SIP ya gaza tabuka wani abun kirki a jihar Adamawa da ma yankin arewa baki daya, duk da irin makudan biliyoyin Naira da shugaban kasa ya amince da warewa shirin, Aisha ta ce ba zata yi magana mai tsawo ba don kar a ce ta fiye surutu, musamman ganin cewar sakataren gwamnatin tarayya ya fito ne daga jihar Adamawa.

Duk lokacin da nayi magana sai a ce na cika surutu, ina sukar gwamnati - Aisha Buhari

Aisha Buhari
Source: Depositphotos

"Ba na son na fasa kwan cewar jiha ta bata amfana daga shirin ba. Daga jihar ne sakataren gwamnatin tarayya ya fito. Nayi shiru don kar jama'a su ce na cika surutu. Na ziyarci Kano kwanan nan kuma na ga wani dattijo mai kimanin shekaru 74 dake sayar da tarkacen kayayyaki, da na tambaye shi nawa ne jarin sa sai ya ce min zai kai N3,000 zuwa N4,000. Kar fa ku manta cewar mun yi alkawarin bawa talakawa futik tallafin N5,000 duk wata," a cewar Aisha.

DUBA WANNAN: Mun yi kura-kurai a zabukan da muka yi - Yari ya yi magana a kan hukuncin kotu (Bidiyo)

Da take magana a kan Uwargida Maryam, Aisha Buhari ta bayyana cewar an ba ta mukamin ne tun farko domin saka wa Kanawa a kan miliyoyin kuri'un da suka zazzaga wa mijinta a zaben shekarar 2015

'Yar asalin jihar Kano, Uwargida Maryam, mata ce ga tsohon alkalin alkalan Najeriya, Jastis Mohammed Lawal Uwais.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel