Akwai yiwuwar 'yan Najeriya 24m za su kamu da cutar tabin hankali - WHO

Akwai yiwuwar 'yan Najeriya 24m za su kamu da cutar tabin hankali - WHO

A shekarar da ta gabata shafin BBC Hausa ya ruwaito cewa, masana kiwon lafiya sun bayyana takaici kan yadda ba a damu a duba hanyoyin magance matsalar da biliyoyin al'umma ke fuskanta ba da ta shafi tabin hankali da dangogin su.

Rahoton hukumar lafiya ta duniya WHO ya bayyana cewa, akwai fiye da 'yan Najeriya miliyan 24 da ke rayuwa cikin barazana ta kamuwa da rashin lafiyar tabin hankali da dangogin su a sakamakon ci gaba da hauhawar karancin hukumomi da kuma kwararrun kiwon lafiya.

Shugaban WHO na duniya; Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus

Shugaban WHO na duniya; Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus
Source: UGC

Hukumar WHO ta fitar da wannan rahoto na gargadi mai razanarwa a ranar Asabar yayin fayyace sakamakon binciken ta na 2018 da bayyana a taron karawa juna sani na gaggawa da ta gudanar cikin birnin Yola na Adamawa.

KARANTA KUMA: Malamai ke da alhakin haifar da rashin nagarta a zaben 2019 ba kungiyar mu ba - ASUU

A sakamakon da hukumar lafiya ta duniya ta bayyana, ta'azzarar rashin lafiyar tabin hankali za ta yi kamari cikin kaso 12.1% na adadin al'umma yayin da ta za ta fi yaduwa musamman a tsakanin al'ummar yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel