NGF: Jigon APC Tinubu yayi kira na musamman ga Gwamna Fayemi

NGF: Jigon APC Tinubu yayi kira na musamman ga Gwamna Fayemi

Mun ji labari cewa babban jagoran jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, ya taya Gwamna Kayode Fayemi, murnar zama sabon shugaban kungiyar Gwamnonin jihohin Najeriya.

Bola Tinubu yace yana da tabbacin cewa Dr. Kayode Fayemi zai yi kokari wajen jagorantar ragamar Gwamnonin kasar nan ganin irin kwarewarsa da sanin aiki da kuma naiwar nagartar aiki.

Tinubu ya bayyana wannan ne a wata wasika da ta fito daga ofishinsa a Ranar Juma’a 24 ga Watan Mayun 2019. Tinubu yayi kira ga sabon shugaban gwamnonin yayi kokari wajen gyara kungiyar NGF.

Tsohon gwamnan na Legas ya nemi gwamnan gwamnonin na yanzu ya dage wajen ganin ‘Yanuwansa sun taimakawa cigaban Najeriya tare da goyon bayan gwamnatin shugaban kasa Buhari.

Wasikar babban ‘dan siyasar ta fara da cewa:

“Ina taya ka murnar zama shugaban gwamnonin Najeriya bayan mubaya’ar da aka yi maka.”

KU KARANTA: Yadda ake maganin tsananin kishin ruwa a Watan azumi

NGF: Jigon APC Tinubu yayi kira na musamman ga Gwamna Fayemi

Tinubu yayi kira ga Gwamna Fayemi ya marawa Buhari baya
Source: Depositphotos

Tinubu yake fadawa Gwamna Fayemi cewa:

“Zaben ka da sauran Gwamnoni Takwarorinka su kayi, ya nuna irin yarda da kai da su kayi domin ka jagoranci al’amuransu na shekaru biyu masu zuwa.”

Asiwaju Tinubu ya bayyana cewa:

“A matsayina na wanda yayi hulda da kai kuma na san ka a cikin ‘yan shekarun nan, ina da tabbaicn cewa za kayi kokari duba da irin tarin kwarewar ka da sanin aiki da kuma Baiwar shugabanci da nagarta da ka ke da ita…”

“…Gwamna da kayi a karon farko da kuma mukamin Minista da ka rike a Abuja, har ka dawo ka sake komawa ofis za su taimaka maka wajen wannan aiki”

“Ina fata da addu’a cewa za kayi kokari wajen yi wa kungiyar NGF gyara domin ta rika bada gudumuwa wajen cigaban Najeriya a kowane bangare musamman harkar tattalin arzikin cikin gida tare da marawa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari baya.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel