Babban Kotu ta hana INEC ta ba Okorocha takardar lashe zaben Sanata

Babban Kotu ta hana INEC ta ba Okorocha takardar lashe zaben Sanata

- An dakatar da Hukumar INEC daga ba Gwamna Rochas Okorocha satifiket

- Kotu tace ka da a ba ‘Dan takarar Sanatan na Imo shaidar lashe zabe tukun

Babban kotun tarayya da ke zama a Garin Owerri da ke jihar Imo ya dakatar da hukumar zabe mai zaman kan-ta watau INEC daga mikawa Rochas Okorocha satifiket da ke nuna cewa ya lashe zaben Sanatan yankin jihar Imo.

Har yanzu dai abubuwa na zuwa ma gwamna Rochas Okorocha da matsala tun bayan zaben Watan Fubrairun 2019 inda Alkali mai shari’a E.F. Njemanze ya nemi INEC ta ajiye maganar ba Okorocha satifiket din nasara tukun.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC ta nada babban Sakatare na rikon kwarya

Babban Kotu ta hana INEC ta ba Okorocha takardar lashe zaben Sanata

Nasarar Gwamna Okorocha a zaben 2019 tana sama tana dabo
Source: Depositphotos

Babban kotun ya fadawa INEC ta koma kan matsayarta bayan a da hukumar ta fara tunanin yin amai ta lashe ta hanyar ba ‘dan takarar Sanatan takardar da ke nuna cewa ya lashe zaben bana, bayan a da can ta hana sa satifiket din cin zabe.

Jones Onyeriri wanda yayi takara da Rochas Okorocha shi ne ya kai kara gaban kotu yana mai kalubalantar nasarar da gwamnan jihar ya samu a zaben 2019 na ‘dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar yankin Imo ta Yamma.

A yanzu kotu tace INEC ta bar maganar ba Okorocha satifiket har sai zuwa lokacin da aka kammala sauraron karar da ake yi a gaban kuliya. Babban Mai shari’a Njemanze ya dage zaman kotu sai Ranar Laraba 5 ga Watan Yunin 2019.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel