Malamai ke da alhakin haifar da rashin nagarta a zaben 2019 ba kungiyar mu ba - ASUU

Malamai ke da alhakin haifar da rashin nagarta a zaben 2019 ba kungiyar mu ba - ASUU

Hukumar malaman jami'o'in Najeriya ASUU, ta barrantar da kanta daga duk wani zargi na sa hannun ta cikin rudani ko kuma rashin nagarta da malamai suka haifar yayin babban zaben kasa na bana a Najeriya.

Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU, ta ce ba bu abinda ya game ta da duk wata tangarda da rashin tangarta da suka auku yayin gudanar da babban zaben kasa na bana a fadin kasar nan.

Shugaban kungiyar ASUU na kasa Farfesa Biola Ogunyemi

Shugaban kungiyar ASUU na kasa Farfesa Biola Ogunyemi
Source: Getty Images

Shugaban kungiyar ASUU na kasa Farfesa Biola Ogunyemi, shi ne ya yi furucin hakan cikin wata sanarwa yayin ganawar sa da manema labarai a karshen mako cikin birnin Awka na jihar Anambra dake Kudu maso Gabashin Najeriya.

Sabanin yadda ake ikirari da shafa mata bakin fyanti, Farfesa Ogunyemi ya tsarkake kungiyar ASUU yayin wata laccar bankwana da kuma kaddamar da littafin tsohon shugaban jami'ar Michael Okpara, Farfesa Ikenne Onyido a jihar Anambra.

Farfesa Ogunyemi ya ce kungiyar ASUU ta tsarkaka daga duk wata tangarda da ta auku yayin gudanar da babban zaben kasa na bana domin kuwa ba ta yi ruwa da tsaki ba wajen tantance Malaman jami'o'i da hukumar zaben ta kasa mai zaman kanta INEC ta dauka a matsayin Turawan zabe.

KARANTA KUMA: Gwamnati za ta kashe N900m a makarantun Almajirai na jihar Kebbi

A yayin da wasu kungiyoyi da dama ke kiran hukumar INEC a kan kauracewa amfani da malaman jami'o'i a matsayin alkalan zabe da za ta gudanar a gaba, kungiyar ASUU ta ce ba ta hurumin haramtawa mambobin ta shiga harkokin gudanar da zabe a kasar nan.

Kungiyar ASUU ta ce a yayin da gazawar malaman jami'o'i ta haifar da wata tangarda yayin sauke nauyin da rataya wuyan su kasancewar Turawan zabe, ba ta da wani hurumi a cikin hakan da a cewar ta ko kadan laifin su ba zai shafe ta ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel