Na sake koma wa garkuwa da mutane ne domin samun kudin biyan lauya na - Mai laifi

Na sake koma wa garkuwa da mutane ne domin samun kudin biyan lauya na - Mai laifi

Watanni bakwai kacal da fitowar sa daga gidan yari bayan samun shi da laifin yin garkuwa da mutane, Sorbari Apollolos ya sake tsintar kan sa a gidan yari bayan sake aikata laifin da kai shi gidan yarin.

Apollolos, wanda da aka fi kira da 'Blackie', tare da ragowar abokan aikin ta'addacinsa sun shiga hannun jami'an rundunar 'yan sanda bayan sun sace tare da yin garkuwa da wata dattijuwar 'yar kasuwa mai suna Obianuju, mai shekaru 67 a dunyia.

An kama Blackie da ragowar abokansa uku; Daniel Johngbo, Harridon Barryira da Lebara Tobia, a wurare daban-daban a jihar Ribas.

A ranar 7 ga watan Fabrairu ne Blackie da ragowar abokansa, dauke da manyan bindigu, suka sace Obianuju tare da yin garkuwa da ita bayan sun yi mata kwanton bauna yayin da take koma wa gida daga Coci a cikin motar ta kirar Toyota Sienna.

Sun tsare ta a cikin jeji na tsawon kwanaki 6 kafin daga bisani su sake ta bayan sun karbi miliyoyi a matsayin kudin fansa.

Na sake koma wa garkuwa da mutane ne domin samun kudin biyan lauya na - Mai laifi

Wasu gungun masu garkuwa da mutane da 'yan sanda suka kama a hanyar Abuja
Source: Facebook

Bayan sun sake ta ne sai dattijuwar ta rubuata takardar koke zuwa ga babban sufeton rundunar 'yan sanda, Mohammed Adamu, wanda ya bawa rundunar IRT umarnin zakulo wadanda suka yi garkuwa da ita.

Jami'an rundunar IRT sun yi nasarar kama Blackie a maboyar sa dake garin Kono-Bowe a karamar hukumar Khana ta jihar Ribas.

DUBA WANNAN: Mayakan Boko Haram sun kashe sojoji 25 a wani harin kwanton bauna

Dattijuwar ta bayyana cewar 'yan ta'addar sun sace ta ne yayin da suke sanye da kakin sojoji.

Da yake magana da manema labarai, Blackie ya bayyana cewar wani maigidansa da ake kira Gbenena, wanda har yanzu 'yan sanda ke nema, ne ya shirya sace Obianuju, tare da bayyana cewar N350,000 ne kason shi daga cikin kudin fansar da aka biya.

Sannan ya kara da cewa an daure shi a gidan yari ne bayan samun sa da laifuka masu nasaba da garkuwa da mutane da fashi da makami, sannan ya bayyana cewar ya amince ya kara aikata laifin yin garkuwa da mutane domin samun kudin da zai biya lauyansa da ya tsaya masa har aka fito da shi daga gidan yari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel