Gwamnati za ta kashe N900m a makarantun Almajirai na jihar Kebbi

Gwamnati za ta kashe N900m a makarantun Almajirai na jihar Kebbi

Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu, ya ce gwamnatin sa ta ware naira miliyan dari tara domin inganta Makarantun Almajirai da babbar manufa ta samar da ilimin addini da kuma na zamani ga manyan gobe.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, lafazin Gwamna Bagudu na zuwa ne yayin wani taron shirin Almajiranci da kungiyoyin makarantun Almajirai da kuma na masu yaki da jahilci suka dauki nauyin gudanar wa cikin Birnin Kebbi a ranar Lahadi.

Gwamnan jihar Kebbi; Abubakar Atiku Bagudu

Gwamnan jihar Kebbi; Abubakar Atiku Bagudu
Source: UGC

Cikin jawaban sa, gwamna Bagudu ya ce "gwamnatin sa za ta ci gaba da kwazo wajen bayar da mafificin tallafi da gudunmuwar inganta harkokin gudanarwa a makarantun Almajirai dake duk wani kwararo da sako a fadin jihar."

Gwamna Bagudu yake cewa "a halin yanzu gwamnatin sa ta hanyar ma'aikatar ilimi ta tanadi Naira miliyan dari tara domin inganta jin dadi da kuma harkokin gudanarwa a dukkanin makaratun Almajirai dake jihar Kebbi."

Ya ce gwamnatin sa za ta bayar da gagarumar gudunmuwa ta inganta jin dadin Malamai a Makarantun Allo da kuma Almajirai ta hanyar samar da wadatattun bandakuna da kuma kayayyaki na karantarwa.

KARANTA KUMA: Hukumar 'yan sanda ta cafke 'yan ta'adda 43 a jihar Bauchi

Kamar yadda gwamna Bagudu ya bayar da shaida, za a fara karantar da Almajirai darussan ilimin zamani kama daga yaren turanci, lissafi, da kuma darussan kimiya da fasaha daidai da tanadi da kuma tsari na ma'aikatar ilimi ta kasa baki daya.

Kazalika gwamna Bagudu ya yabawa kwazon uwargidan sa Hajiya Aisha Bagudu, da ta assassa shirin gidauniyar nan ta MALPAI (Mass Literacy Programme and Almajiris Initiative) domin inganta rayuwar Almajirai da kuma yaki da jahilci a fadin jihar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel