Mun yi kura-kurai a zabukan da muka yi - Yari ya yi magana a kan hukuncin kotu

Mun yi kura-kurai a zabukan da muka yi - Yari ya yi magana a kan hukuncin kotu

Gwamnan jihar Zamfara mai barin gado, Abdulaziz Yari, ya amince da hukuncin koli tare da bayyana cewar tabbas sun yi kura-kurai a zabukan fidda 'yan takara da suka gudanar a jihar.

Da yake jawabi yayin taron shan ruwa na karshe da ya shirya wa kwamishinoni da kusoshin gwamnatin jihar Zamfara a gidansa dake Talata Mafara, Yari ya ce abinda ya faru kaddara ce daga ubangiji, a saboda haka ya rungumi kaddara.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne kotun koli ta yanke hukuncin soke kuri'un da dukkan 'yan takarar APC suka samu a jihar Zamfara a zabukan da aka kammala bayan tabbatar da cewar jam'iyyar ba ta gudanar da zabukan cikin gida bisa doron doka ba.

Mun yi kura-kurai a zabukan da muka yi - Yari ya yi magana a kan hukuncin kotu

Abdulaziz Yari
Source: Twitter

Kazalika, kotun ta bayyana 'yan takarar jamiyyar PDP da suka zo na biyu a matsayin wadanda suka samu nasarar lashe zabe a dukkan kujerun da suka yi takara a jihar Zamfara.

"Haka Allah ya tsara, dole mu yarda da hukuncin ubangiji. Imanin mutum ba ya cika sai ya amince da kaddara me kyau ko akasin haka," a cewar Yari.

DUBA WANNAN: Boko Haram sun kashe sojoji 25 da dumbin farar hula a wani harin kwanton bauna

Gwamnan ya taya zababben gwamnan da zai gaje shi murna tare da yi masa fatan alheri da addu'ar Allah ya bashi ikon yin adalci.

"Allah ya yi musu jagora yadda jihar Zamfara za ta amfana, mutanen jihar ma su amfana daga mulkin su," inji Yari.

Kalli faifan bidiyon jawabin gwamnan da ake ta yada wa a dandalin sada zumunta da kafafen yada labarai:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel