Ma'aikata sun yiwa Gwamna Yari bankwana a jihar Zamfara

Ma'aikata sun yiwa Gwamna Yari bankwana a jihar Zamfara

Bayan shafe tsawon shekaru takwas a kan gadon mulki, a ranar Asabar da ta gabata ma'aikatan gwamnati a jihar Zamfara, sun yiwa gwamna Abdulaziz Yari bankwana yayin liyafar shan ruwa da buda bakin azumi da aka gudanar.

Shugaban kungiyar kwadago reshen jihar Bashir Marafa, a gidan gwamna Yari dake karamar hukumar Talata Mafara, ya yabawa kwazon gwamnan a sakamakon inganta ci gaba da jin dadin al'umma cikin tsawon shekaru takwas da ya shafe a karagar mulki.

Gwamnan jihar Zamfara; Abdulaziz Abubakar Yari

Gwamnan jihar Zamfara; Abdulaziz Abubakar Yari
Source: Twitter

Cikin kalaman sa Bashir ya ce mai girma Gwamna Yari ya yi kwazon gaske da gagarumar bajinta marar iyaka da ta yi tasiri wajen kulla kyakkyawar dangartaka ta hadin kai a tsakanin ma'aikatan gwamnati a jihar Zamfara.

A yayin da ya nemi gwamna Yari akan sauke nauyin bashin albashin ma'aikata gabanin ya mika akalar jagoranci a mako mai zuwa, Marafa ya yabawa kwazon gwamnan musamman yadda a kwana-kwanan nan ya sauke nauyin bashin Naira biliyan biyu na masu karbar fansho a jihar.

KARANTA KUMA: Yadda yanayi zai kasance cikin manyan birane a Najeriya

A madadin dukkanin ma'aikatan jihar Zamfara, shugaban kungiyar ta kwadago ya yi addu'ar samun nagartaccen magaji da kuma fatan alheri ga Gwamna Yari yayin barin kujerar sa ta jagoranci.

Cikin nasa jawaban, kakakin majalisar dokoki na jihar Zamfara Alhaji Sanusi Rikiji, ya yi addu'ar neman Mai Duka ya sanya shamaki a tsakanin Gwamna Yari da dukkanin ababen sharri tare da neman dukkanin magoya bayan jam'iyyar APC a kan hadin kai a tsakanin su da juna.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel