Abin da nasarar Zamfara ta ke nufi wurin Atiku – Jam’iyyar PDP

Abin da nasarar Zamfara ta ke nufi wurin Atiku – Jam’iyyar PDP

- Jam’iyyar PDP tana sa ran za ta yi nasara a karar zaben shugaban kasa na 2019

- Sakataren yada labarai na PDP ya bayyana wannan ne bayan shari’ar Zamfara

Jam’iyyar PDP mai adawa ta taya ‘yan takararta da ke jihar Zamfara murnar nasarar da su ka samu a kotun koli a Ranar Juma’ar da ta gabata. Sakataren yada labaran jam’iyyar, Kola Ologbondiyan, shi ne ya aika wannan sako.

Mista Kola Ologbondiyan yake cewa muna-munar da hukumar INEC ta rika shiryawa a jihar Zamfara bai kai ga ci ba, bayan da kotu tayi watsi da shirin hukumar. Kotun koli dai ta rushe duk kuri’un da APC ta samu a zaben bana.

Sakataren yada labaran jam’iyyar yake cewa Atiku Abubakar, wanda ya rikewa PDP tuta a zaben shugaban kasa na bana, zai yi nasara a gaban kotun da ke sauraron karar zabe kamar yadda PDP ta samu nasara a Zamfara.

KU KARANTA: An roki Kotu ta hana ‘Dan APC neman takarar kujerar Majalisar Tarayya

Babbar jam’iyyar hamayyar tayi wannan jawabi ne a Ranar Asabar 25 ga Watan Mayu ta bakin Kakakin na ta domin taya Bello Matawalle da sauran ‘yan takarar ta masu jiran rantsarwa murnar gagarumar nasarar da su kayi.

PDP tace: "Yayin taya 'Yan takarar PDP murnar lashe kujerun jihar Zamfara, mu na kuma sa rai cewa gaskiya za tayi halin ta a shari'ar da ake yi da Atiku Abubakar a Kotu bayan murde zaben 2019. Atiku zai karbe mulki a kotu."

A karshe jam'iyyar tana kira ga hadin kai inda tace

"Jihar Zamfara tana albarkatu da-dama a ban kasa da kuma tarin al'umma, don haka gwamnati mai zuwa za tayi kokari wajen ganin an maida hankali yadda jama'a za su amfana da baiwar da Allah ya ba su."

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

-

Source: Legit

Mailfire view pixel