Ciki da waje da kan rufi: Mutum miliyan 3.2 sun yi sallar Taraweeh a masallacin Annabi a Ramadana

Ciki da waje da kan rufi: Mutum miliyan 3.2 sun yi sallar Taraweeh a masallacin Annabi a Ramadana

Wata kididdiga da hukumar kasar Saudiyya ta fitar ta bayyana cewar fiye da mutum miliyan 3.2 sun gudanar da sallar dare ta musamman (Taraweeh) da ake yi cikin watan Rammadana a masallacin manzon Allah dake birnin Madinah.

A cikin sanarwar da ta fito daga ofishin shugaban kula da masallatan Saudiyya masu tsarki guda biyu, ta bayyana cewar adadin mutanen sun yi salla a masallacin ne a cikin kwanaki 15 na farkon azumin watan Ramadana.

Sanarwar ta kara da cewa a kalla mutane kimanin miliyan 1.4 sun gudanar da sallar a cikin masallacin yayin da kimanin mutane miliyan 1.5 suka gudanar da tasu sallar a cikin harabar masallacin da kuma wasu mutane fiye da dubu 230 da suka gudanar da tasu a kan rufin masallacin.

Ciki da waje da kan rufi: Mutum miliyan 3.2 sun yi sallar Taraweeh a masallacin Annabi a Ramadana

Masallacin Annabi a Madinah
Source: UGC

A kalla mutum 15,623 ne ke gudanar da sallar Taraweeh a masallacin ko wacce rana, 98,589 a cikin masallacin da kuma wasu 100,868 a harabar masallaci da makwabatn gine-gine.

DUBA WANNAN: Buhari ya sha ruwa da masu bukata ta musamman, ya zuba musu abinci da hannun sa (Hotuna)

Kimanin masu aikin Umrah 669,048 sun ziyarci kabarin Annabi (tsira da aminci su tabbata a gare shi) da kuma sahabbansa biyu; Abu Bakr da Umar, tare da yin sallama a kabarinsu dake daf masallacin.

Miliyoyin musulmi daga sassa daban-daban na duniya kan yi tururuwar tafiya kasar Saudiyya a cikin watan azumi domin gudanar da aikin Umrah tare da gabatar da bukatar su ga ubangiji ta hanyar yin addu'o'i na musamman don neman tubaraki da alfarmar dake cikin watan Ramadana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel