Zango na biyu: Buhari ya bar ministoci cikin zulumi

Zango na biyu: Buhari ya bar ministoci cikin zulumi

A yayin da ya rage saura kwanaki kasa da biyar a sake rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin zababben shugaban kasar Najeriya a karo na biyu, ministocin sa sun kara kaimi wajen matsin lamba da kamun kafa a wurin makusanta shugaba Buhari domin a sake koma wa gwamnati da su.

Rahotanni sun bayyana cewar a kalla kaso 70% na ministocin Buhari sun bar aiyukan su domin cigaba da shige-da-ficen ganin sun samu koma wa kujerun su. Sai dai wata majiya a fadar shugaban kasa ta bayyana cewar ministocin sun shiga kamun kafa ne saboda sun san cewar wannan karon shugaba Buhari ba zai dauki dogon lokaci ba wajen nada ministocin da zasu taya shi aiki.

Majiyar ta bayyana cewar shugaba Buhari zai jingine batun nan na tsuke yawan mukaman ministoci kamar yadda ya yi a zangon shi na farko.

"Bayan ministoci 36 da shugaban kasar zai nada; mutum guda daga kowacce jiha, ana saka ran cewar zai kara wasu ministocin guda 6; mutum daya daga kowanne yanki 6 na kasar nan.

"Bisa ga dukkan alamu, shugaban kasa ba zai bata lokaci ba wajen nada sabbin mukamai ba. A shirye yake ya aika sunayen sabbin ministocin da zai nada zuwa majalisa a watan Yuni don ya zuwa yanzu ya riga ya san mutanen da zai yi aiki da su a zangon sa na biyu," a cewar majiyar.

Zango na biyu: Buhari ya bar ministoci cikin zulumi

Buhari da ministoci
Source: UGC

Sannan majiyar ta kara da cewa babu wanda ya san sunayen su waye shugaba Buhari zai aike majalisa, hakan ne kuma ya tayar da hankalin ministocin sa na yanzu suka shiga kamun kafar na kusa da shi da kuma shugabancin jam'iyya.

A cewar majiyar, wannan karon shugaba Buhari zai raba ma'ikatar aiyuka, lantarki da gidaje zuwa ma'aikatu uku; ma'aikatar aiyuka, ma'aikatar lantarki da ma'aikatar gidaje, domin a samu damar gudanar da aiki a kowacce ma'aikata cikin sauki.

DUBA WANNAN: Zango na farko: Abinda yasa ban taba rushe ministoci ba - Buhari

Kazalika ana saka ran cewar shugaban kasar zai fitar da ma'aikatar harkokin jiragen sama (Aviation) daga cikin ma'ikatar sufuri tare da mayar da ita ma'aikata mai cin gashin kan ta.

Saidai, a yayin da shugaba Buhari ya yi taron mazalisar zartarwar tarayya (FEC) da ministocin a cikin da ya wuce, shugaban kasar ya shaida wa ministocin cewar su cigaba da aiki har zuwa ranar 28 ga watan Mayu, jajiberin ranar sake rantsar da Buhari.

Buhari ya sanar da ministocin cewar a yayin da suka koma ofis don cigaba da aiki, su kuma cigaba da shirin mika aiki ga manyan sakatarorin ma'aikatun da suke jagoranta a ranar 28 ga watan Mayu

Tuni kafafen yada labarai suka fara wallafa rahotanni dake dauke da wasu sunayen ministoci da aka tabbatar da cewa shugaba Buhari ba zai koma da su ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel