Fastocin Arewa sun ce Buhari bai da kudirin Musuluntar da Najeriya

Fastocin Arewa sun ce Buhari bai da kudirin Musuluntar da Najeriya

- Shugaban kungiyar fastocin arewa, Bishop Abu Richard, a soki zargin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin Musuluntar da Najeriya

- Bishop Abu Richard yace ba shugaban kasar bane ya haddasa kashe-kashe a kasar

- Malamin yayi kira ga yan Najeriya Musulmi da Kirista da su ci gaba da addu’a domin samun gwamnati mai inganci a shekaru hudu masu zuwa

Shugabannin addini karkashin kungiyar Fastocin Arewa a ranar Asabar, 25 ga watan Mayu sun ba Kiristoci tabbacin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai musuluntar da Najeriya ba.

Tabbacin martani ne ga furucin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yayi inda yake zargin Buhari da kokarin Musuluntar da kasar baki daya.

Shugaban kungiyar fastocin arewa, Bishop Abu Richard yayinda yake jawabi ga manema labarai akan taron addu’an kafin ratsar da Buhari wanda ya gudana a Abuja yace ba shugaban kasar bane ya haddasa kashe-kashe a kasar.

Fastocin Arewa sun ce Buhari bai da kudirin Musuluntar da Najeriya

Fastocin Arewa sun ce Buhari bai da kudirin Musuluntar da Najeriya
Source: UGC

Richard yayi kira ga yan Najeriya Musulmi da Kirista da su ci gaba da addu’a domin samun gwamnati mai inganci a shekaru hudu masu zuwa karkashin Buhari.

KU KARANTA KUMA: Matasan Najeriya akwai hazaka kwarai da gaske, inji Buhari

Malamin wanda yan nuna bakin ciki kan garkuwa da mutane da sace-sacen mutane a kasar, ya shawarci Buhari da hukumomin tsaro da su daidaita lamarin don guje na rikici.

Ya kuma yaba da taruwansu domin shirinsu na zaman lafiya da jajircewa wajen hadin kan kasa.

Daga karshe ya kuma shawarci kungiyar Kiristocin Najeriya da su yi tafiya da dukkanin kiristoci a ayyukan kungiyar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel