Kotu ta taba samun Gbajabiamila da laifi a 2007 – An fadawa Kotu

Kotu ta taba samun Gbajabiamila da laifi a 2007 – An fadawa Kotu

Mun samu labari cewa an roki wani babban kotun tarayyar Najeriya da ke zama a birnin Abuja ta hana Honarabul Femi Gbajabiamila neman takarar kujerar shugaban majalisar wakilan tarayya.

A karar mai lamba na FHC/ABJ/CS/539/2019, an fadawa kotu cewa Femi Gbajabiamila bai cancanci ya rike wani ofis ba tun daga ‘dan majalisar wakilai har ga zuwa kakakin majalisar kasar.

Philip Undie, wanda shi ne ya shigar da karar, ya fadawa kotu cewa an taba samun ‘dan majalisar da laifi a kasar Amurka a shekarar 2007, don haka yace bai dace a bar shi ya rike babban ofis ba.

Daga cikin wadanda ake tuhuma a wannan kara akwai majalisar wakilan tarayya, Ministan shari’an Najeriya da kuma jam’iyyar APC mai mulki. Har yanzu dai ba a zabi wanda zai saurari karar ba.

KU KARANTA: Jerin 'Yan takarar PDP da su ka lashe zabe a sama a Zamfara

Kotu ta taba samun Gbajabiamila da laifi a 2007 – An fadawa Kotu

Hon. Femi Gbajabiamila a lokacin wani zama a zauren Majalisa
Source: UGC

A wannan kara da aka shigar a Ranar Laraba 22 ga Watan Mayu, an fadawa kotu cewa an taba tuhumar Femi Gbajabiamila da damfarar wasu Bayin Allah kudi har $25000 a lokacin yan kasar waje.

Undie yayi wa kotu wannan bayani ne ta bakin Lauyansa Mister Ayodele inda yace kotu ta taba samun Gbajabiamila da laifi lokacin yana aikin Lauya a Garin Georgia da ke jihar Atlantan Amurka.

Wannan ya sa aka nemi kotu ta bada umarni cewa Hon. Femi Gbajabiamila ya tashi daga matsayin ‘dan majalisar Najeriya har ma ta kai yana hankoron kujerar shugaban majalisar wakilan tarayya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel