Fusatattun matasa sun kone wani dan fashi a birnin Abuja

Fusatattun matasa sun kone wani dan fashi a birnin Abuja

- Wasu fusatattun matasa a birnin Abuja sun kone wani shugaban 'yan fashi da suka kama

- Yan fashin sun shiga wata unguwa a cikin Abuja da misalin karfe 1 na dare suka dinga yiwa mutane fashi har zuwa karfe 3

An cafke wani mutumi wanda ake zargin dan fashi da makami ne, ranar Juma'a da safe, inda aka sanya masa taya aka kunna masa wuta a unguwar Lugbe dake Zone 9 a cikin birnin Abuja.

Mun samu rahoton cewa 'yan fashin wadanda suka kai kimanin su tara, sun shiga unguwar da misalin karfe 1 na dare suka fara yiwa mutane fashi har zuwa karfe 3 na dare.

Fusatattun matasa sun kone wani dan fashi a birnin Abuja

Fusatattun matasa sun kone wani dan fashi a birnin Abuja
Source: Facebook

Daga baya an gano shugaban 'yan fashin, wanda ya umarci yaran nashi da su gudu.

A cewar wani wanda lamarin ya faru a kan idonshi, ya ce bayan sun gama fashin nasu, daya daga cikin 'yan fashin yayi kokarin kwace shugaban nasu, wanda wani mutumi ya kama. Inda shi kuma shugaban nasu ya umarce su akan su gudu su kyaleshi, a tunanin shi zai kubuta.

KU KARANTA: Manyan alkalai mata guda 8 da sunayen manyan 'yan siyasa da suke aure

"Daya daga cikin wadanda suka yiwa fashin ya jefi shugaban 'yan fashin da dutse, hakane yasa suka samu nasarar kamashi. Sun karya mishi kafa, sannan suka sanya mishi wuta suka kone shi." in ji shaidar.

Wani babba a yankin ya bayyana cewa mutanen unguwar sun kira jami'an 'yan sanda akan su zo su dauke gawar dan fashin bayan sun kone shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel