EFCC taki cewa komi kan zargin da ake yiwa Tinubu

EFCC taki cewa komi kan zargin da ake yiwa Tinubu

-Yan Najeriya na cigaba da ganin gazawar hukumar EFCC wajen fara gudanar da binciken da ya shafi tsohon gwamnan Legas Bola Tinubu.

Hukumar yaki da cin hanci da kuma zangon kasa na tattalin arziki ta EFCC a ranar Alhamis ta karyata da ke yawo cewa ta fara gudanar da bincike akan tsohon gwamnan jihar Legas Bola Tinubu.

‘Yan Najeriya na cigaba da matsa lamba ga hukumar ta EFCC kan cewa ai lallai ta binciki Tinubu saboda ana tuhumarsa da almundahanar kudade, wanda ake zargin an kawo masa gidansa cike da mota biyu a ranar 22 ga watan Fabrairun 2019.

EFCC taki cewa komi kan zargin da ake yiwa Tinubu

Bola Tinubu
Source: Facebook

KU KARANTA:Kurun kus! gaskiya tayi halinta a jihar Zamfara, inji Atiku

Wannan zance ya haifar da cece kuce musamman da yake abin ya faru ne ana saura kwana daya zaben shugaban kasa wanda akayi ranar 23 ga watan Fabrairu.

Tinubu dai na hannun daman Buhari ne kowa ya sani, Buhari kuma shi ne dan takarar neman shugabancin kasa a karo na biyu karkashin jam’iyar APC.

Masu yin suka na cewa ko shakka babu wadannan motocin da suka shiga gidan Tinubu kudi suka kawo masa domin ayi amfani da su wurin sayen kuri’u, saboda motocin ana amfani da sune musamman saboda daukar kudi na banki ko kuma na gwamnati.

Tsohon gwamnan jihar Legas ya amsa cewa tabbas kudi ne aka kawo masa cikin motocin amma dai ba na abinda mutane ke tunani bane.

Da dama cikin yan Najeriya na jira su ga matakin da EFCC zata dauka akan lamarin. Sai dai kuma hukumar yaki da cin hanci da zagon kasa na tattalin arziki taki cewa uffan akan lamarin.

Hakan ne ma ya haifar da zargi musamman daga wurin daidaikun mutane, cewa hukumar EFCC ta gaza binciken Tinubu ne saboda yana tare da gwamnati mai ci a yanzu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel