Ta tabbata: PDP ce ka da Jihar Zamfara - INEC

Ta tabbata: PDP ce ka da Jihar Zamfara - INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na Kasa (INEC) ta bayyana dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a jihar Zamfara.

Wannan ya biyo bayan soke kuri'un jam'iyyar APC da kotun koli tayi ne.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayar da wannan sanarwar a ranar Asabar 25 ga watan Mayu.

Yakubu ya ce za a bawa wadanda suka lashe zaben shedan cin zabe a ranar Litinin.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya taya Modi murnar lashe zabe

Mr Mutawalle ne ya zo na biyu a zaben gwamna da aka gudanar a watan Maris a jihar amma yanzu shine zababen gwamnan jihar saboda hukuncin kotun koli na soke kuri'un jam'iyyar APC domin ba su gudanar da zabukkan cikin gida ba kamar yadda dokokin jam'iyya ya tananda.

Hakan na nufin dukkan wadanda suka zo na biyu a zabukan majalisa za su zama zababun 'yan majalisa a yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel