Ganduje ya ware makudan kudade domin gyaran kwatami a Kano

Ganduje ya ware makudan kudade domin gyaran kwatami a Kano

-N119m ne kudin da gwamnatin Kano ta ware domin kariya daga aukuwar ambaliya a jihar ta hanyar gyaran kwatami.

-Dakta Ali Makoda kwamishinan muhalli na jihar shi ne ya bada wannan sanarwa a ranar Asabar bayan ya zagaya domin ganin aikin tsaftar muhalli na wata-wata.

A ranar Asabar ne gwamnatin jihar Kano tace ta ware naira miliyan 119 domin yashe duk kwatamin dake birnin jihar don kariya daga ambaliya.

Kwamishinan muhalli na jihar, Dakta Ali Makoda shine ya bada wannan sanarwa a ranar Asabar bayan ya kammala zagayen duba tsaftace muhalli da akeyi a ko wane wata.

Ganduje ya ware makudan kudade domin gyaran kwatami a Kano

Ganduje ya ware makudan kudade domin gyaran kwatami a Kano
Source: Twitter

KU KARANTA:Kurun kus! gaskiya tayi halinta a jihar Zamfara, inji Atiku

Makoda yace, gwamnatin Ganduje na da manufar tabbatar da cewa jama’ar Kano sun samu muhalli mai matukar tsafta.

“ A dalilin hakan ne ya sanya ake yashe kwatamin duk shekara.” Kamar yadda ya fadi. Duk da cewa gwamnati na kokari a nata bangaren akwai bukatar jama’ar gari su taimaka domin ganin an samar da tsaftataccen muhalli a jihar.

Makoda wanda yace wannan ne zagayensa na karshe domin ganin yadda aikin tsaftace muhallin ke gudana, a matsayin shi na kwamishinan muhalli ya jinjinama jama’a bisa goyon bayansu wajen tsaftar muhallin.

Ya kuma yabawa yan jarida saboda wayar da kai da sukeyi ga jama’a akan muhimmancin tsaftar muhalli. Saboda yan jarida na kasancewa tsakanin jama’a da gwamnati musamman wurin isar sakonni.

Makoda a karshe, ya nemi duk wanda zai shigo a matsyin sabon kwamishinan muhalli da ya dada zage damtse wurin ganin cigaban wannan kyakkyawan aiki na gyaran muhalli.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel