Abubuwan da yakamata ku sani game da ‘Singham’

Abubuwan da yakamata ku sani game da ‘Singham’

-Hakika Singham zai bar jama'a da kewa yayin da yayi ritaya daga aikin dan sanda.

-Singham yayi ritaya daga aikin dan sanda a ranar Juma'a 24 ga watan Mayun 2019 kwanaki biyu kacal kafin cikarsa shekaru 60 a duniya.

Taken dan sanda abokin kowa ya dace da Wakili ganin yadda jama’a ke bayyana yadda yake baiwa kowa girmansa daidai gwargwado tun daga kan jami’an yan sanda har zuwa jama’ar gari.

Wakili shi ne dan sandan da jama’a ke bin ayarin motocinsa bisa kyakkyawan zato da su keyi masa akan kamanta gaskiya da yake, kamar yadda tawagar BBC ta shaida yayin wata ziyara da ta kai masa a ofishinsa.

Abubuwan da yakamata ku sani game da ‘Singham’

CP Wakili 'Singham'
Source: Twitter

KU KARANTA:Kurun kus! gaskiya tayi halinta a jihar Zamfara, inji Atiku

Muhammad Wakili dan sanda ne mai kwarjini wanda ya yi fice kwarai da gaske a Najeriya musamman inda ake yabon shi da kamanta gaskiya.

A yanzu haka dai, dan sanda ya yi murabus daga aiki a ranar Juma’a 24 ga watan Mayun 2019, kwanaki biyu kafin cikarsa shekaru 60 da haihuwa.

A sakamakon hazakar da yake nunawa wurin aiki ta sanya jama’ar gari suka yi mashi lakabi da ‘Singham’ wanda suna ne ga wani jajirtaccen dan sanda a wani fim na Indiya.

Ganin yadda wannan sunan da aka lakaba masa ya bi duniya shi da kansa Wakilin ya aminta da a rika kiransa da wannan suna.

Muhammad Wakili dai ya fara yin fice a Najeriya ne tun bayan yaduwar wani bidiyonsa a shafukan sada zumunta inda yake nuna kiyayya ga fatauci da kuma shan miyagun kwayoyi a tsakanin al’umma.

Bayanai sun nuna cewa yakin da Wakili yake akan fatauci da kuma shan miyagun kwayoyi da gaske yake, saboda ya kama dillalan kwayoyi da dama a lokacin aikinsa.

Amma kash! A daidai lokacin da tauraruwarsa ke haskawa ya rage masa saura makwanni kadan yayi ritaya daga aikin dan sanda.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel