Sabbin masarautun Kano: Kungiyar matasa da dalibai sun yabawa Ganduje

Sabbin masarautun Kano: Kungiyar matasa da dalibai sun yabawa Ganduje

Kungiyar Daliban Jihar Kano, NAKSS da Kungiyar Matasa na Kasa, NYCN, sun yabawa Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano saboda kirkiran sabbin masarautu hudu a Jihar Kano.

Kungiyoyin sunyi wannan yabon ne a yayin da suka kai ziyarar ban girma ga sabbon sarkin Bichi, Aminu Ado Bayero ranar Juma'a a fadarsa.

A yayin da ya ke magana a madadin kungiyoyin, Shugaban NYCN a Kano, Kabiru Ado-Lakwaya ya ce sun kai ziyara domin ban girma ga sabbon sarkin mai daraja ta daya da kuma nuna goyon bayan su ga sarkin.

Sabbin masarautun Kano: Kungiyar matasa da dalibai sun yabawa Ganduje

Sabbin masarautun Kano: Kungiyar matasa da dalibai sun yabawa Ganduje
Source: Twitter

A cewarsa, kirkiran sabbin masarautun hudu abin farin ciki ne da zai inganta rayuwar al'ummar masarautan.

DUBA WANNAN: Hukuncin Zamfara: Ba mu da zabi sai dai mu amince da hukuncin kotu - APC R

Mr Lakwaya ya kara da cewa zai kai ziyarar ban girma ga sauran sabbin sarakunan.

A jawabinsa, Sarkin ya bukaci matasa a Kano su kasance wakilan jihar na gari a duk inda suka samu kansu ta hanyar riko da tarbiyar addinin musulunci.

Ya kuma shawarci matasan su guji aikata ayyukan masha'a domin su samu damar bayar da gudunmwarsu wurin cigaban jihar da kasa baki daya.

Sarki Bayero ya ce matasa ne manyan gobe saboda haka ya kamata su kasance masu nuna halaye na gari da za su inganta garuruwansu.

Basaraken ya kuma shawarci matasa da daliban su cigaba da biyaya ga dokoki domin kawar da muggan ayyuka a kasa.

Ya kuma tabbatar musu cewa ba za a bar kowa a baya ba wurin gudanar da ayyukan cigaba a garruwan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel