Gini ya ruguzo wa 'yan makaranta a Ondo, daya ta rasu

Gini ya ruguzo wa 'yan makaranta a Ondo, daya ta rasu

An shiga dimuwa a makarantar St Andrew Grammar School da ke garin Ondo a ranar Juma'a sakamakon rushewar gini da ya yi sanadiyar rasuwar daliba guda daya.

An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a lokacin karatu kuma malamai da dalibai sunyi gaggawan ficewa daga dakunan karatu da ofisoshi domin su tallafawa marigayiyan.

An gano cewa dalibar da ta rasu, Esther Akinrinola mai shekaru 14 a duniya tana aji uku ne na karamar sakandire.

Ginin makaranta ya ruguzo a kan daliban firamare a Ondo

Ginin makaranta ya ruguzo a kan daliban firamare a Ondo
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Manyan jaruman Kannywood uku sun samu wata babban kwangila

Wata majiya ta ce an dade da dena amfani da ginin amma ya ruguzo ne lokacin da dalibai ke wasa ciki.

Ya ce, "Suna wasa ne cikin kagon yayin da katanga ya fado a kan dalibar da ta rasu. Ta mutu ne a kan hanyar zuwa Asibitin koyarwa na Ondo inda ake nufin zuwa yi mata magani."

Ya ce an fara gudanar da bincike a kan lamarin.

Ya ce shugaban makarantar ya ce an dena amfani da ginin na tsawon lokaci amma ba mu gamsu ba saboda haka akwai yiwuwar za a tuhumi shugaban makarantar da laifin sakaci.

"Tunda an dena amfani da ginin, mene yasa suka kyalle dalibai suna wasa a kusa da ginin?

"Rushe ginin ya dace ayi. Mun fara bincike a kan lamarin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit Newspaper

Online view pixel