An soke hawan sallah a jihar Katsina

An soke hawan sallah a jihar Katsina

- Sanadiyyar yawan kashe-kashe da yayi yawa a jihar Katsina, Sarkin Katsina ya sanar da soke hawan sallah a fadin jihar

-Sarkin yace za a fita sallar idi amma ba za ayi shagulgulan sallah ba, saboda nuna jimami ga wadanda suka rasa rayukan su

Masarautar garin Katsina ta fitar da wata muhimmiyar sanarwa, inda a cikin sanarwar ta aika da sakon ta'aziyya ga dukkanin al'ummar jihar akan ibtila'in da ya faru na kashe mutanen garin Batsari, Dan Musa, Kankara da Wagini da sauran garuruwa da lamarin ya shafa.

An soke hawan sallah a jihar Katsina

An soke hawan sallah a jihar Katsina
Source: UGC

Sakataren masarautar garin Katsinan Alhaji Bello M IFO shine ya fitar da sanarwar, inda ya shaidawa al'umma cewa sakamakon yanayin da al'ummar jihar suka tsinci kansu na jimami da alhini, masarautar ta yanke shawarar ba zata gabatar da hawan sallah ba a wannan karon.

KU KARANTA: Rundunar sojin sama tayi nasarar kashe 'yan Boko Haram masu yawan gaske a wani hari da ta kai sansanin su

Alhaji Bello ya bayyana cewa Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Dr. Abdulmumin Kabir Usman CFR, da 'yan majalisarsa suka ga ya dace a soke duk wasu harkokin shagulan biki domin su nuna jimamin su akan abinda ya faru ga al'ummar jihar.

A karshe sanarwar ta bayyana cewa za aje ayi sallar idi kamar yadda aka saba, sannan za ayi addu'o'i na neman zaman lafiya ga jihar ta Katsina da ma kasa baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel