Rundunar sojin sama tayi nasarar kashe 'yan Boko Haram masu yawan gaske a wani hari da ta kai sansanin su

Rundunar sojin sama tayi nasarar kashe 'yan Boko Haram masu yawan gaske a wani hari da ta kai sansanin su

- A wani hari da rundunar sojin sama ta kai, ta samu nasarar tarwatsa wasu gungun 'yan ta'adda a kan iyakar tafkin Chadi

- Rundunar ta kai harin ne bayan ta samu rahoton maboyar 'yan ta'addar a wani daji dake kusa da iyakar tafkin Chadi

Rundunar sojin saman ta 'Operation Lafiya Dole ta ce takai wani mummunan hari ga wani sansanin 'yan Boko Haram, a wani kauye mai suna Tumbun Hamma dake kan iyakar Tafkin Chadi.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ya fitar a yau Asabar dinnan, ya bayyana cewa sun kai harin ne bayan wani rahoto da jami'an leken asiri suka kai musu, sun tabbatar da cewar sun ga 'yan ta'addar wadanda suka gudu yayin da rundunar sojin sama ta hadin gwiwa suka kai musu hari a kusa da Malkanori-Tumbun Rego dake yankin arewacin jihar Borno.

Rundunar sojin sama tayi nasarar kashe 'yan Boko Haram masu yawan gaske a wani hari da ta kai sansanin su

Rundunar sojin sama tayi nasarar kashe 'yan Boko Haram masu yawan gaske a wani hari da ta kai sansanin su
Source: UGC

Sanarwar ta kara da cewa, an kai harin ne bayan sun tabbatar da rahoton da 'yan leken asirin suka tabbatar akan wurin da 'yan ta'addar suke, bayan kai harin rundunar ta tabbatar da kashe 'yan ta'addar masu dumbin yawa a sansanin nasu, inda gawarwakin su suka cika yankin da rundunar ta kai harin.

KU KARANTA: Yadda rikicin jam'iyyar APC ya samo asali a jihar Zamfara

Matsalar ta'addanci dai taki ci taki cinyewa a Najeryia, duk kuwa da irin kokarin da hukumomin tsaro suke yi na ganin sun kawo karshen matsalar a fadin kasar.

Matsalolin tsaron da suke addabar Najeriya sun hada da matsalar 'yan ta'addar Boko Haram, 'yan bindiga, barayin shanu, masu garkuwa da mutane da kuma matsalar matsafa masu shan jini, wadanda suka addabi jihonin, Borno, Yobe, Adamawa, Kaduna, Katsina, Zamfara da dai jihohi da dama a fadin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel