Babu wanda ya yi korafin cewa na sace masa kudi - Patience Jonathan

Babu wanda ya yi korafin cewa na sace masa kudi - Patience Jonathan

Patience, uwargidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, a ranar Juma'a ta bukaci babban kotun tarayya da ke Legas ta mayar mata da $5.7m da N2.4bn da Hukumar Yaki da masu yiwa arzikin kasa ta'annti, EFCC ta kwace daga hannunta.

Lauyan ta, Cof Ifedayo Adedipe (SAN) ya bukaci Mai shari'ah Mojisola Olatoregun ya yi watsi da bukatar hukumar EFCC ne neman a mikawa gwamnatin tarayya kudaden da aka kwace daga hannun Patience.

Adedipe ya ce kuskure na EFCC tayi tsamanin cewa kudin sata ne tunda ba samu Patience da aikata wani laifi ba kuma babu wanda ya yi korafin cewa kudadensa sun bata.

Babu wanda ya yi korafin cewa na sace masa kudi - Patience Jonathan

Babu wanda ya yi korafin cewa na sace masa kudi - Patience Jonathan
Source: UGC

Ya ce an bawa Patience kyautan kudaden ne lokacin da mijinta ke shugabancin Najeriya.

Adedipe ya ce dama an saba bawa mutane irin wannan kyautan.

DUBA WANNAN: Zamfara ta cika da murna bayan hukuncin kotun koli a kan APC

Ya ce sashi na 17 na dokar masu damfarar kudi da EFCC da dogara ta ida wurin kwace kudaden Patience yana magana ne a kan 'yan damfara.

Ya ce, "Ba doka ba ne EFCC da rika bibiyar asusun mutanen da ba ta kaunar fuskokinsu ta rika cewa kotu ta kwace kudadensu.

"Gwamnati na da ikon kwarbe kudade daga hannun mutane amma sai a bayyana laifin da ya janyo daukan matakin."

Adedipe ya ce babu dalilin da zai sa a kwace kudaden a bawa gwamnatin tarayya tunda EFCC ba ta gabatar da hujojin da ke nuna cewa kudin na sata ba ne.

"Abinda EFCC tayi kawai ta ga kudi a asusun ta ne sai tayi tsamanin cewa na sata ne. Ba ta fadi daga inda aka sato kudin ba."

Justice Olatoregun ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Yuni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel