Gobara tayi barna a sansanin ‘yan gudun hijira guda 2 dake Borno

Gobara tayi barna a sansanin ‘yan gudun hijira guda 2 dake Borno

-Gobara ta auku a sansanin 'yan gudun hijira wanda shine na biyu a girma a jihar Borno.

-A sanadiyar wannan gobara rumfuna 38 ne suka kone kurumus sakamakon hakan mazauna wannan sansani suka shiga halin takura.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno tace rumfuna 38 ne wuta lamushe a sansanin ‘yan gudun hijira guda biyu dake karamar hukumar Ngala ta jihar Borno.

Daraktan hukumar bayar da agajin mai inkiya da SEMA, Malam Usman Kachalla shine ya sanar da aukuwar wannan lamari ranar Juma’a a Maiduguri yayin wata zantawa da kamfanin dillacin labarai na kasa NAN.

Gobara tayi barna a sansanin ‘yan hijira guda 2 dake Borno

Gobara tayi barna a sansanin ‘yan hijira guda 2 dake Borno
Source: Twitter

KU KARANTA:‘Yan sanda sun kama soja hudu da wasu mutane 84 akan zargin aikata fashi da makami

Kachalla yace, rumfuna 38 ne suka kone hakan yayi sanadiyar wargatsewar jama’ar dake sansanin a ranar 21 ga watan Mayu da gobarar ta auku.

Yace, gobarar ta soma ne daga wani tanti dake cikin sansanin a saboda rashin yan kwana-kwanan da zasu kashe wutar sai da ta keyawa sansanin tare da yin barna mai yawa.

Ya kara da cewa, hukumar tasu da takwarorinta na iya bakin kokarinsu ganin cewa sun baiwa jama’ar sansanin tallafin da suke bukata.

Sansanin na Ngala shine na biyu a girma a jihar Borno inda yake dauke da ‘yan gudun hijira mutum 14,000.

Ta’addacin da yankin ke fama da shi tuni ya tsallaka kasashen dake makwabtaka da Najeriya kamar su Nijar, Chadi da Kamaru, wanda ya janyo hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaron kasashen domin fada da ta’addancin.

Kungiyar Boko Haram ta kasance tana addabar Najeriya tun shekarar 2009 a lokacin da tayi yinkurin kafa gwamnatin musulunci zalla.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel