Yadda rikicin jam'iyyar APC ya samo asali a jihar Zamfara

Yadda rikicin jam'iyyar APC ya samo asali a jihar Zamfara

- A jiya ne wata kotin koli ta soke zaben jam'iyyar APC na jihar Zamfara

- Kotun ta kuma kwace kujerar gwamnan jihar daga hannun jam'iyyar APC ta mikawa jam'iyyar PDP

- Hakan ne yasa zamu kawo muku ainahin abinda yaa hurawutar rikicin jam'iyyar APC a jihar ta Zamfara

Jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ta jihar Zamfara ta kasu kashi biyu ne, wato bangaren gwamna mai barin gado Abdul'aziz Yari da kuma bangaren mataimakinsa da Sanata Kabiru Marafa da Ministan tsaro da kuma Hon Jaji.

Wutar rikicin siyasar jihar ta samo asali ne a lokacin da gwamnan jihar Abdulaziz Yari ya nuna goyon bayansa ga kwamishinan kudin jihar, Alhaji Muktar Shehu Idris, inda ya nuna cewa shine zai hau kujerar gwamnan jihar idan ya sauka.

Hakan ne ya janyo jam'iyyar APC a jihar ta kasa yin zaben fidda gwani na 'yan takarar gwamna dana 'yan majalisar tarayya da kuma na 'yan majalisar jiha.

Yadda rikicin jam'iyyar APC ya samo asali a jihar Zamfara

Yadda rikicin jam'iyyar APC ya samo asali a jihar Zamfara
Source: Facebook

Wannan dalilin ne yasa wasu manya a jihar masu sha'awar fitowa takarar gwamna a jam'iyyar APC kimanin su takwas kamar irin su mataimakin gwamnan jihar Ibrahim Wakalla da ministan tsaro na kasa Mansur Dan Ali suka hada kai guri guda domin su yaki gwamnan.

Sau kusan biyu ana kokarin gabatar da zaben fidda gwani a jihar, amma a karshe sai a soke zaben saboda rikicin dake tsakanin bangarorin jam'iyyar guda biyu.

A bangaren gwamnan jihar, ya fake da wani sakamakon hukunci da babbar kotun jihar ta yanke, inda alkalin kotun ya bayyana cewa an gabatar da zabe ba tare umarnin hukumar zabe ta kasa ba.

Hukuncin da wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta yanke, shine ya tabbatar da matsayin hukumar zabe ta kasa akan haramta wa dukkanin 'yan takarar jam'iyyar APC na jihar yin zabe.

Hukuncin da kotun Abujan ta yanke yayi daidai dana kotun jihar wanda mai shari'a Muhammad Bello Shinkafi ya yanke.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Jonathan ya samu sabon mukami

Sai dai kuma alkalin kotun tarayyar mai shari'a Ijeoma Ojukwu ta jaddada matsayin hukumar zabe na kasa, inda ta bayyana cewa jam'iyyu za su cigaba da yin karen-tsaye akan dokokin zabe idan har suka kasa mutunta ka'idojin da aka kafa na jadawalin zabe.

Alkalin ta ce hukunci da aka yanke din darasi ne ga sauran jam'iyyun kasar nan a nan gaba.

Bayan an daga zaben 2019 ne wata kotu dake Abuja ta bai wa hukumar INEC umarnin karbar 'yan takarar APC, hakan ne yasa jam'iyyar APC a Zamfara ta shiga zaben 2019.

Sai dai kuma wata kotun daukaka kara a jihar Sokoto ta yi watsi da hukuncin kotun Abuja, inda hakan ne yasa bangaren gwamnati ya daukaka kara zuwa kotun koli.

Yanzu haka dai kotun koli ta soke zaben jam'iyyar APC na jihar baki daya.

Akwai alamun irin hakan za ta faru a jihar Kano, inda yanzu haka ake sauraron karar da dantakarar gwamnan jihar na jam'iyyar PDP Abba Kabir Yusuf ya shigar, inda yaake neman kotu ta binciki zaben jihar akwai lauje cikin nadi, musamman ma ganin yadda aka dage zaben wasu kananan hukumomi a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel