An tsaurara matakan tsaro domin karbar bakuncin Buhari a Ogun

An tsaurara matakan tsaro domin karbar bakuncin Buhari a Ogun

Shugaba Muhammadu Buhari ya isa Abeokuta babban birnin jihar Ogun inda zai kaddamar da wasu ayyuka da Gwamna Ibikunle Amosun ya yi.

Gabanin zuwan shugaban kasar an tsaurara tsaro a garin Abeokuta da wasu sassan jihar inda shugaba Buhari zai kai ziyara domin kaddamar da wasu ayyuka.

Buhari zai kaddamar da wasu ayyuka da gwamna mai barin gado Sanata Ibikunle Amosun ya yi a jihar wadanda aka yiwa lakabi da 'Legacy Projects.'

Daily Trust ta ruwaito cewa an baza jami'an tsaro a muhimman wurare musamman Kobape, Oke-Mosan, Kuto da Oke-Ilewo inda mafi yawancin ayyukan da za a kaddamar su ke.

An tsaurara matakan tsaro domin karbar bakuncin Buhari a Ogun

An tsaurara matakan tsaro domin karbar bakuncin Buhari a Ogun
Source: Twitter

An tsaurara matakan tsaro domin karbar bakuncin Buhari a Ogun

An tsaurara matakan tsaro domin karbar bakuncin Buhari a Ogun
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Manyan jaruman Kannywood uku sun samu wata babban kwangila

Wasu daga cikin ayyukan da ake sa ran kaddamarwa sun hada da; Ofishin ma'aikatn shari'a da ke kan titin Kobape a Amphi-Theatre da kuma tsohon gidan gwamnati da aka yiwa kwaskwarima a Oke-Ilewo.

Saura sun hada da asibiti na zamani mai gado 250 a Oke-Mosan, filin tashin jirage na kasa da kasa da ke karamar hukumar Ewekoro da gidan talabijin na zamani mallakar jihar Ogun da ke Ajebo road.

Ana sa ran shugaban kasar zai isa Abeokuta misalin karfe 9.50.

Tuni dai gwamnatin jihar ta soke tsafattace muhullai na watan Mayu da ya dace ayi a yau.

Sanarwar da kwamishinan muhalli, Bolaji Oyeleye ya fitar ya ce, "an soke tsaftace muhallin ne saboda ziyarar shugaba Muhammadu Buhari inda zai kaddamar da 'Legacy Projects' a sassan jihar."

Kwamishinan ya bukaci dukkan 'yan jihar su fito suyi maraba da shugaban kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel