'Yan sanda sun kama makiyaya da laifin fyade da kissar gilla a Delta

'Yan sanda sun kama makiyaya da laifin fyade da kissar gilla a Delta

Mazauna garin Ebu da ke jihar Delta sunyi nasarar kama wasu makiyaya fulani biyu da ke ake zargi da kai farmaki ga jama'ar garin a ranar Juma'a 24 ga watan Mayu.

An gano cewa an kama wadanda ake zargin ne a kasuwar Eke da ke garin Ebu saboda zarginsu da ake yi da yiwa wasu matan aure fyade da kuma kashe wasu mazauna garin.

An mika wadanda ake zargin a hannun 'yan sandan yankin Illah inda aka sake garzayawa da su zuwa hedkwatan 'yan sanda da ke Asaba domin sunyi ikirarin mai gidansu yana zaune ne a Asaba.

'Yan sanda sun kama makiyaya da laifin fyade da kissar gilla

'Yan sanda sun kama makiyaya da laifin fyade da kissar gilla
Source: UGC

DUBA WANNAN: Zamfara ta cika da murna bayan hukuncin kotun koli a kan APC

Kakakin 'yan sandan jihar, DSP Onome Onuvuwakpoyeya ya tabbatarwa manema labarai kama makiyayan, inda ya kuma ce za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike.

Daya daga cikin mazauna garin, Cif Ebewe John ya shaidawa manema labarai cewa "mazauna garin sun gudanar da taro na musamman inda suka dauki matakin binciko makiyayan da suka zo garin suka tafka abin kunya ba tare da an san sun zo garin ba. Hakan yasa aka bawa matasa umurnin su kamo su a kasuwar Eke."

Cif John ya yi kira ga gwamnatin jihar ta dauki mataki kare jama'ar jihar daga hare-haren makiyaya domin kare barkewar rikici a jihar inda ya kara da cewa su mutane ne masu son zaman lafiya amma ba za su amince wasu baki su shigo garinsu su rika tayar da zaune tsaye ba.

Mazauna garin sun dade suna ikirariin cewa an yiwa matansu fyade yayin da wasu suka ce 'yan bindiga dauke da muggan makamai suna yawo suna kashe jama'a a garin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel