Za a sanya tara ga masu yin bahaya a titi a jihar Kano

Za a sanya tara ga masu yin bahaya a titi a jihar Kano

- An sanya tarar naira dubu uku ga duk babban mutumin da aka kama yana bahaya a wani kauye na jihar Kano

- Sannan za a dinga cin yara kanana tarar naira dubu biyu, inda iyayensu zasu dinga biya ga duk wanda aka kama yana yin bayan gida a wurin da bai dace ba

Wani kauye mai suna Yammawar Kafawa, wanda ke karkashin hukumar UNICEF, ya mayar da yin bayan gida akan titi laifi, kuma zai dinga cin tarar duk mutumin da aka kama da wannan laifin.

Rabiu Usman, shugaban kauyen, shine ya bayyana hakan ga manema labarai a lokacin da suka kai ziyara kauyen, wadda hukumar UNICEF tare da ma'aikatar labarai da al'adu ta kasa.

Manema labaran sun bayyana cewa ziyarar tana daya daga cikin kokarin ganin an tsaftace Najeriya ta hanyar wayarwa da mutane kai akan amfani da bandaki.

Za a sanya tara ga masu yin bahaya a titi a jihar Kano

Za a sanya tara ga masu yin bahaya a titi a jihar Kano
Source: Facebook

Usman ya yabawa hukumar UNICEF da irin kokarin da take yi gurin ganin ta tsaftace mahallan mutane da kuma ruwan sha, ya bayyana cewa mutanen kauyen sunyi rungumi al'adar tsaftace muhallin hannu biyu-biyu, ta hanyar wanke bayan gidansu, da kuma wanke hannayensu bayan sun gama bayan gida.

Ya bayyana cewa an sanya tara ne akan duk mutumin da aka kama domin ganin mutane sun kara rungumar abin hannu biyu-biyu.

"Mun saka tarar naira dubu uku akan duk wani mutum da muka kama yana bahaya a fili.

KU KARANTA: Tsohon shugaban kwallon kafa na kasa, ya shiga layin 'yan takarar gwamnan jihar Kogi

"Sannan mun saka tarar naira dubu biyu ga kananan yara. Iyayen yaran ne zasu biya kudin, sannan kuma duk wanda aka kama zai kwashe bahayan da hannunshi." in ji Usman.

Mai garin kuma yace ya sanya mutane kullum suna zagayawa ko zasu ga wani wanda zai karya dokar.

"Har ya zuwa yanzu dai bamu kama ko mutum daya da ya karya dokar ba," in ji mai garin.

A karshe mai garin ya shawarci sauran garuruwa da su bi sahu irin nasu, domin tsaftace muhalli da kuma samun lafiya mai dorewa ga al'umma baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel