Hukuncin Zamfara: Ba mu da zabi sai dai mu amince da hukuncin kotu - APC

Hukuncin Zamfara: Ba mu da zabi sai dai mu amince da hukuncin kotu - APC

- Ntufam Hillard Eta, mataimakin shugaban APC na kasa reshen Kudu maso Kudu ya ce jam'iyyar za ta amince da hukuncin kotun koli a Zamfara saboda ba ta da wani zabin

- Eta ya ce jam'iyyar mai mulki tana da darussa sosai da za ta koya daga abinda ya faru a Zamfara tun daga lokacin zabukan cikin gida

- Jigon na jam'iyyar na APC ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a Abuja bayan taron kwamitin gudanarwa na jam'iyyar

Zamfara: Ya zama dole mu amince da hukuncin kotu - Jam'iyyar APC

Zamfara: Ya zama dole mu amince da hukuncin kotu - Jam'iyyar APC
Source: Depositphotos

Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa reshen Kudu maso Kudu, Ntufam Hilliard Eta ya ce jam'iyyar mai mulki ba ta da wani zabi sai dai ta amince da hukuncin da kotun koli da zartar na soke nasarar da tayi a zaben gwamna da 'yan majalisun jihar da tarayya a jihar Zamfara.

Eta ya yi wannan jawabin ne yayin zantawa da manema labarai bayan taron kwamitin gudanarwa a akayi a sakatariyar jam'iyyar a Abuja. Ya ce akwai darussan da jam'iyyar za ta koya daga abinda ya faru a Zamfara.

DUBA WANNAN: Zamfara ta cika da murna bayan hukuncin kotun koli a kan APC

A yayin da ya ke tsokaci kan hukuncin, ya ce, "ranar bakin ciki ne ga kowa a jam'iyyar APC. Ranar bakin ciki ne sosai gare mu dukka."

Da aka tambaye shi ko yana ganin jam'iyyar APC ta warware matsalar yadda ya dace, ya ce, "Bana tunanin jam'iyya ba ta dauki matakan da suka da ce ba a jihar Zamfara. Ba mu da wani zabi sai dai mu amince da hukuncin kotun koli kuma akwai darrusan da zamu koya daga hukuncin. Wannan shine abinda zan iya fada a yanzu."

Wadanda suka hallarci taron na kwamitin gudanarwar sun hada da zababen gwamnan jihar Yobe, Mallam Mala Buni da sakataren jam'iyyar na kasa mai barin gado.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel