Hukuncin jihar Zamfara: Shugabannin jam'iyyar APC sun shiga ganawar sirri

Hukuncin jihar Zamfara: Shugabannin jam'iyyar APC sun shiga ganawar sirri

Wata ganawar sirri na shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kan gudana a yanzu a sakatariyar jam'iyyar dake unguwar Wuse2, birnin tarayya Abuja.

Jaridar Daily Trust ta bada rahoton cewa ana ganawar ne kan hukuncin da kotun kolin Najeriya ta yanke na fatali da dukkan kuri'un jam'iyyar APC a jihar Zamfara.

A bangare guda, Shugaban kwamitin man fetur a majalisar dattawan Najeriya, Kabiru Marafa, a ranar Juma'a ya siffanta hukuncin da kotun kolin Najeriya kan yan takaran jam'iyyar APC matsayin abu mai dadi kuma mara dadi, amma nasara ce ga siyasa, jihar Zamfara, da kasa ga baki daya.

Marafa wanda ya yi wannan jawabi a matsayin dan tsokaci kan hukuncin kotun ya ce "komin daren dadewa, gaskiya za tayi nasara kan karya"

Marafa yace: "Hukuncin ranar Juma'a nasara ce ga demokradiyya, nasara ga gaskiya kuma tabbatar da cewa kotu ce mafi gaskiya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel