APC: INEC tayi magana kan hukuncin kotun koli a Zamfara

APC: INEC tayi magana kan hukuncin kotun koli a Zamfara

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC, ta ce za ta bayyana matsayar ta kan hukuncin da kotun koli ta yanke na soke kuri'un 'yan takarar jam'iyyar APC a Jihar Zamfara yayin babban zaben 2019.

Hukumar ta ce ta kira taron gaggawa domin tattaunawa kan hukuncin da kotun ta zartas.

"INEC za ta sake zama goba Asabar 25 ga watan Mayun 2019 domin cigaba da tattaunawa a kan batutuwan da suka taso sakamakon hukuncin kotun kolin, amma sai ranar Litinin 27 ga watan Mayu ne za mu fitar da matsayar mu," a cewar sanarwar da kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu zabe na INEC, Festus Okoye ya fitar.

APC: INEC tayi magana kan hukuncin kotun koli a Zamfara

APC: INEC tayi magana kan hukuncin kotun koli a Zamfara
Source: UGC

DUBA WANNAN: Akwai tartsatsin harsashi a idon Sheikh El-Zakzaky - ICRP

Da farko, Legit.ng ta kawo muku cewa kotun kolin Najeriya ta yanke hukuncin cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba tada hakkin takara a zaben gwamnan jihar kuma saboda haka, an yi fatali da dukkan kuri'un da ta samu.

Gamayyar alkalai biyar na kotun sun yi ittifaki a ranar Juma'a cewa jam'iyyar APC bata gudanar da zaben fidda gwani ba bisa ga ka'idojin jam'iyyar.

Babban alkali, Paul Adamu Galinji, ya ce dukkan kuri'un da aka kadawa jam'iyyar APC banza ne kuma an jam'iyyar da tazo na biyu a zabubbukan ne zababbun masu kujerar.

Tunda al'amari ya zama haka, jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP da yan takararta da kuma jam'iyyun da suka zo na biyu a zaben za'a nada matsayin gwamnan jihar, yan majalisar dokoki, na wakilai da na dattawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel