Dankari: An damke matashi da matashiya suna lalata bayna nasi cikin watan Ramadan

Dankari: An damke matashi da matashiya suna lalata bayna nasi cikin watan Ramadan

Hukumar yan sandan farin hula wato NSCDC, ta alanta damke wasu matasa biyu a garin Maiduguri, jihar Borno kan jima'i a bainar jama'a cikin watan Ramadan mai albarka.

Kwamandan hukumar, Abdullahi Ibrahim, ya bayyanawa manema labarai a ranar Juma'a cewa an damke wadannan matasa ne ranar Alhamis, 23 ga wata a unguwar Abbaganaram a Maiduguri.

Mista Abdullahi ya laburta cewa matashin dan shekara 20 ne kuma yarinyar yar shekara 17 ce.

Ya ce jami'ansa sun damkesu ne bayan wani jami'in JTF wanda ya gansu suna lalata bayna naasi.

KU KARANTA: Hukuncin kotun koli nasara ce ga Demokradiyya - Sanatan APC, Kabiru Marafa

Kwamandan ya kara cewa matashinya bayyana cewa ya zabi yin lalata a waje ne saboda bai da kudin kama Otal.

Ya bada tabbacin cewa za'a gurfanar da su a kotu muddin aka kammala bincike kan al'amarin.

A wani labarin, Hukumar Hizbah, shiyar jihar Kebbi, ta ceto wata jaririyar yar kwanaki biyu da haihuwa bayan mahaifiyarta ta birneta da rai.

An gano gawar yar jaririyar kwana biyu bayan haihuwarta a bayan wani Otal dake cikin garin Birnin Kebbi.

Mahaifiyar yarinyar da wata kawarta sun kama daki a shahrarran Otal mai suna Zinari, na tsawon kwana biyu kuma suka silale suka birne yarinyar cikin dare a bayan Otal.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel