Kurun kus! gaskiya tayi halinta a jihar Zamfara, inji Atiku

Kurun kus! gaskiya tayi halinta a jihar Zamfara, inji Atiku

-Atiku ya furta kalmomin yabo ga kotun koli ta Najeriya bisa yanke hukunci da tayi akan zaben jihar Zamfara wanda ya baiwa jam'iyarsa ta PDP nasara.

Dan takarar shugabancin Najeriya karkashin jam’iyar PDP Atiku Abubakar yace kotun koli ta tabbatar da adalci, biyo bayan hukuncin da ta yanke wanda ya baiwa Bello Matawalle damar kasancewa sabon gwamnan jihar Zamfara.

“ Babu abinda ya fi dadi a kunnuwan masu imani kamar jin wannan hukuncin adalci da kotun ta yanke cikin watan Ramadana mai alfarma.” Kamar yadda Atiku ya fadi ta hanyar hadiminsa Paul Ibe.

Kurun kus! gaskiya tayi halinta a jihar Zamfara, inji Atiku

Kurun kus! gaskiya tayi halinta a jihar Zamfara, inji Atiku
Source: Twitter

KARANTA WANNAN:Yan Najeriya na fadin albarkacin bakinsu bisa hukunci kotun koli akan zaben Zamfara

Atiku ya yabawa alkalan da suka yanke wannan hukunci, “ bisa namijin kokarin ganin cewa ba’a tauye gaskiya ba ko kadan, saboda sun dubi kudurin yan Najeriya da ma kasar baki daya.”

“ Allah Ya kasance farko, sannan kasarmu Najeriya, haka yakamata ace duk wani dan Najeriya mai nagarta ya kasance.

“ Bayan da gaskiya ta bayyana, jama’a sun cika da farin ciki, yayin da kowa ke sambarka da aukuwar wannan lamari.” Kamar yadda ya fadi.

Kuma ya ce, “ ina fatan wannan kotu mai adalci zata yi irin adalcin da ta saba yi a shari’u masu zuwa gareta nan gaba, ta hanyar jin tsoron Allah da kuma yin adalci.”

Idan sukayi hakan, sunansu ba zai gogu ba a tarihi, ya kuma dada jinjina da yabo ga kotun koli akan wanzar da wannan hukuncin mai cike da adalci.

A karshe ya taya sabon gwamnan murnar samun wannan nasara, tare da ilahirin jama’ar jihar Zamfara wadanda a yanzu suka samu gwamnan da zai share masu kukansu.

“ Rikici ya kau, yanzu Zamfara zata sake samun zaman lafiyan da aka santa da shi. Allah Ya albarkaci kotun koli, jihar Zamfara da kuma kasar Najeriya.” Inji Atiku.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel