Da duminsa: Masari ya amince da hukuncin kisa a kan masu garkuwa da mutane

Da duminsa: Masari ya amince da hukuncin kisa a kan masu garkuwa da mutane

Gwamna Aminu Masar na jihar Katsina ya rattaba hannu kan dokar hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane ko satar shanu a jihar Katsina.

Kazalika, an ya kuma amince da zartar da hukuncin zaman gidan yari na har abada ga wadanda aka samu da aikata fyade baya ga diyyar kudi da za a bawa wanda aka yiwa fyaden.

Wannan dokokin suna zuwa ne a lokacin da ake samun yawaitar hare-haren 'yan bindiga a garuruwa uku a Dan Musa, Faskari da Batsari wadda ya yi sanadiyar rasuwar mutane 26.

Da duminsa: Masari ya amince hukuncin kisa a kan masu garkuwa da mutane

Da duminsa: Masari ya amince hukuncin kisa a kan masu garkuwa da mutane
Source: UGC

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace Direkan Kannywood

Sakamakon harin da aka kai na kwana-kwanan nan, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da Gwamna Masari kuma ya bukaci shugabanin hukumomin tsaro su gudanar da bincike kan kashe-kashen.

Shugaba Buhari ya umurci sufeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Abubakar Adamu da Shugaban hafsoshin tsaro, Janar Abayomi Gabriel Olonisakin su kafa wata kwamitin bincike a jihar kuma su kawo masa rahato.

Shugaban kasan ya ce shugabanin hukumomin tsaron su gano yadda aka shirya kai harin cikin wannan watan Ramadana mai albarka sannan su dauki matakan kare afkuwar hakan a gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel