Hukuncin kotun koli nasara ce ga Demokradiyya - Sanatan APC, Kabiru Marafa

Hukuncin kotun koli nasara ce ga Demokradiyya - Sanatan APC, Kabiru Marafa

Shugaban kwamitin man fetur a majalisar dattawan Najeriya, Kabiru Marafa, a ranar Juma'a ya siffanta hukuncin da kotun kolin Najeriya kan yan takaran jam'iyyar APC matsayin abu mai dadi kuma mara dadi, amma nasara ce ga siyasa, jihar Zamfara, da kasa ga baki daya.

Marafa wanda ya yi wannan jawabi a matsayin dan tsokaci kan hukuncin kotun ya ce "komin daren dadewa, gaskiya za tayi nasara kan karya"

Marafa yace: "Hukuncin ranar Juma'a nasara ce ga demokradiyya, nasara ga gaskiya kuma tabbatar da cewa kotu ce mafi gaskiya."

"Kamar yadda muka sani jam'iyyar APC bata samu daman gudanar da zaben fidda gwani a jihar Zamfara ba sakamakon ta'addancin Yari da yan bangan siyasarsa."

KU KARANTA: Yan Najeriya na fadin albarkacin bakinsu bisa hukunci kotun koli akan zaben Zamfara

Saboda haka, wannan ya zama darasi na cewa bin doka da oda kadai zai ciyar da kasar nan gaba kamar yadda shugaba Muhammadu Buhari yake fada."

"Wannan hukunci na nuna cewa shugaban kasa ya yi gaskiya kan rashin sanya baki cikin harkokin wasu sassan gwamnati"

"Ya kara zurfafa mutuncinsa cikin yan Najeriya da duniya na kauracewa duk kokarin da AbdulAziz Yari yayi na ganin cewa ya sa baki."

Mun kawo muku rahoton cewa Kotun kolin Najeriya ta yanke hukuncin cewa jam'iyyar All Progressives Congress APC ba tada hakkin takara a zaben gwamnan jihar kuma saboda haka, an yi fatali da dukkan kuri'un da ta samu.

Gamayyar alkalai biyar na kotun sun yi ittifaki a ranar Juma'a cewa jam'iyyar APC bata gudanar da zaben fidda gwani ba bisa ga ka'idojin jam'iyyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel