An samu rabuwar kai a majalisar zartarwa ta kasa, inji Amaechi

An samu rabuwar kai a majalisar zartarwa ta kasa, inji Amaechi

Majalisar zartarwa bata cinma matsaya guda ba akan yadda tsarin kamfanin jiragen sama mallakar kasa Najeriya zai kasance, inji Rotimi Amaechi.

Rotimi Amaechi yace an samu rabuwar kawuna a tsakanin mambobin majalisar zartarwa ta kasa akan wane kamfani yakamata ya kula da sabon jirgin saman kasa na Nigeria Air wanda gwamnatin tarayya ke kokarin dawowa da shi.

Da yake magana ranar Alhamis bayan kammala ganawar majalisarsu ta zartarwa, tsohon gwamnan Ribas Rotimi Amaechi yace har yanzu maganar dawo da jirgin sama mallakar kasa na nan daram.

An samu rabuwar kawuna a majalisar zartarwa ta kasa, inji Amaechi

Rotimi Amaechi, ministan sufuri
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Yan Najeriya na fadin albarkacin bakinsu bisa hukunci kotun koli akan zaben Zamfara

“ A kan wannan batun, majalisarmu ta rabu kashi biyu. Akwai wadanda ke son gwamnati ta sanya kudi ta farfado da jiragen daga baya kuma ta saida domin cin riba.” A cewarsa.

“ Akwai kuma wadanda ke ganin cewa a’a ba zuba jari yakamata ayi ba domin a sayar, kamata yayi tun fari gwamnati ta nemi wadanda zasu rike kamfanin da sunan Nigeria Airways.”

“ A nan muka tsaya a halin yanzu. Amma maganar cewa za’a bude Nigeria Airways na nan ba muyi watsi da ita ba.” Inji Rotimi.

Gwamantin tarayya ta kaddamar da wannan aiki ne a Farnborough dake Landan a watan Yulin 2018 da niyyar fara aiki a watan Disamban shekarar 2018.

Karamin ministan sufuri Hadi Sirika ne ya sanar da dakatar da wannan aiki ta hanyar amfani da shafinsa na twitter.

“ Ina mai nadamar sanar da ku cewa, majalisar zartarwa ta kasa ta dakatar da shirye-shiryen kaddamar da jiragen saman kasa Najeriya. Mun gode da irin goyon bayan da ku ke bamu.” Kamar yadda ya rubuta a shafinsa na twitter.

Da yake karin haske akan lamarin, ministan yada labarai Lai Muhammad yace matsalar kudi ce ta sanya aka dakatar da wannan aiki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel