Madalla: Shugaba Buhari ya gabatar da sallar Juma’a a babban masallacin kasa

Madalla: Shugaba Buhari ya gabatar da sallar Juma’a a babban masallacin kasa

- Bayan wasu yan shekaru, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, 24 ga watan Mayu ya gabatar da sallar Juma’a a babban masallacin Abuja

- Hakan na daga cikin shirye-shirye da aka tsara domin bikin rantsar da Shugaban kasar a karo na biyu

- Za a rantsar da shugaban kasar a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu a Eagle Square Abuja

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, 24 ga watan Mayu ya gabatar da sallar Juma’a a babban masallacin kasar da ke birin tarayya Abuja.

Sallar na musamman na daga cikin shirye-shirye da aka tsara domin bikin rantsar da Shugaban kasar a karo na biyu.

A lura cewa za a rantsar da Buhari a karo na biyu a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu a Eagle Square Abuja.

Idan za atuna Shugaban kasar ya daina zuwa saar Juma’a a masallacin Abuja yan shekaru da suka gabata.

KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya na fadin albarkacin bakinsu bisa hukunci kotun koli akan zaben Zamfara

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Kungiyar Kiristocin Naajeriya (CAN) ta yi Allah wadai da yunkurin gwamnatin tarayya na samar da lasisin kafa tashar radiyo na Fulani tsantsa.

Fasto Bayo Oladeji, mataimaki na musamman ga Shugaban kungiyar Samson Ayokunle, yace yunkurin ya tabbatar da furucin da aka alakanta da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo game da shirin mayar da kasar kan akidar Fulani da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ke yi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel